yadda ake hada madarar gari ta waken suya

YADDA AKE HADA MADARAR GARI TA WAKEN SUYAAssalamu alaikum dafatan duk muna cikin koshin lafiya a yau nakawo maku hanyoyi guda biyu dazaku wajen hada garin madara na waken suya yana da dadi sosai, mace zata iya yi yazama suna amfani dashi a gida ko kuma ta kulla tana saidawa kunga riba biyu kenan, yana da dadi sosai.


HANYA TA FARKO

ABUBUWAN DA ZA'A NEMA

waken suya mudu 1

Sugar mudu 1

Milk flavour na gari



YADDA ZA'A HADA.

D farko zaki gyara waken suyan ki wanke sai ki shanya shi ya bushe bayan ya bushe sai ki soyashi sama sama in a very low heat, zakiji yana kamshi kuma zaiyi brown soyan wa shi zai rage mai ghafi,saiki hada sugar ki kai wajen nika, anika maki yayi laushi sosai, in ankawo sai ki tankade shi kizuba milk flavour, shikuma sauran tsakin da kika tankade zaki iya kaishi a kara nikawa kunga riba biyu kenan.shikenan garin madara na soya milk ya kammalu..



HANYA TA BIYU.

ABUBUWAN DA ZAA NEMA

Waken suya

Gyada

Sugar

Milk(optional)



YADDA ZA'A HADA..

Da farko za asamu waken suya a wanken shi don fitar datti/kuran da ke cikin shi sai a shanyashi a rana in ya bushe sai soya shi ya yayi dan brown haka, shima gyadar zaa gyarashi a soyashi acire bayan, sai a hada waken suya da gyadar akai wajen nika a nika shi sosai yayi laushi, bayan andawo dashi daga wajen nika sai a samu sugar a daka shi ya daku yay laushi sai ayi mix dinshi da garin waken soya/gyada a hade ya hadu sosai, shikenan garin madarar waken soya tazama ready, zaki iya sa garin madara in kina so, ko milk flavour..

Wasu basa wanken wake soya dinsu, amma kusani wankewa shine yafi kyau don bakusan inda waken suya din ya futo ba

Post a Comment

Previous Post Next Post