WANNE DALILINE YAKESA MATA KE GANIN FARIN RUWA YANA FITO MUSU KAFIN KO BAYAN GANIN PERIODDIN SUSHIN HAKAN

WANNE DALILINE YAKESA MATA KE GANIN FARIN RUWA YANA FITO MUSU  KAFIN KO BAYAN GANIN PERIOD
DIN SU

SHIN HAKAN YANA NUFIN AKWAI MATSALA NE TATTARE DA HAKAN KO BABU
✓Normally mafi yawan mata suna samun fitowar farin ruwa a gabansu throughout menstrual circle dinsu.

✓Akalla mata dayawa suna ganin farin ruwa mai kauri ko salala, mara launi yana fito musu a kowace rana, adadin daya kai kimanin cikin shokalin shayi. Launin ruwan yana iya sauyawa daga farin madara, zuwa farin ruwa, ko kuma baki baki (brown).

✓Banbancin launin ruwan ko kaurin sa yana ta allaqa ne da hormonal changes na jikin ta a lokacin da yake fitowa.

✓Wannan fitan farin ruwa da mace take gani ta gaban ta kafin period dinta normal ne, babu matsala tattare da hakan. Process ne da ake kira "Leukorrhea" Wani lokacin yana iya kasance wa yellowish.

✓Hakan yana faruwa ne sbd yawan hormones "progesterone" dayake taruwa ajikin ta. A wannan gaban ana kiran yanayin da "luteal phase"

✓Wa'ennan hormones kamar su"progesterone" "oestrogen" "androgen" etc sauyin yanayin sune ajikin ta shike sawa tayi ta ganin "vaginal discharge" yana fito mata.

✓ Idan "estrogen" ne sukayi yawa ajikin ta a lokacin, se ruwan ya kasance fari fari, mai yauki
kuma ruwa ruwa.

✓ Idan kuma "progesterone" ne sukayi yawa ajikin ta, se ruwan ya kasance farin madara kuma mai kauri kauri.

✓Koma ya launin ruwan ya kasance, fari ne, ruwa ruwa ne, madara madara ne, yana da kauri ko akasin haka, muddin baya wari ko qarni, gaban mace baya zafi, kaikayi ko radadi, to wannan normal ne.

✓Aikin sa (ruwan) shine yayi flushing duk wani dattin vagina, wasu harmful germs, etc da kuma ya sa vagina ta zama moist all the time. Hakan yana nuna alamar the vagina and the reproductive system is healthy and functional.

SHIN WASU LOKUTA NE ZAKI TSAMMANCI GANIN FARIN RUWA A GABANKI; IDAN KINGANI BA DAMUWA BANE

✓Normally mata suna iya samun bushewar gaba kamar na kwana 3 zuwa 4 kowane bayan yankewar period dinsu. bayan wannan kwanakin, farin ruwa mai danqo yakan sake bullowa wanda zayyi kamar kwana 4 zuwa 5 Kafin ovulation, alama ce ta eggs sun fara developing. ana kiran shi da "follicular phase" that means a lokacin ne "eggs" (for ovulation) suke kokarin girma.

✓Idan kuma lokacin ovulation yayi, ruwan se ya
canza daga mai danqo zuwa fari mai yauki kuma mara kauri (salala) haka. A wannan lokacin yana kara yawa sosai fiye da na kullum a da. Shi kuma ana kiran shi "egg white".

Aikin sa shine ya taimaka wajen santsin sperm a vagina da cervix domin ya samu daman isowa kwai da yake jiransa for ovulation.

✓Sannan Mata dayawa suna amfani da ganin wannan ruwan a matsayin alama ta ovulation dinsu, hakan yana taimaka musu wajen samun ciki da wuri ko kuma kaura cewa yin cikin. Wannan process din shi ake kira da "natural family planning" ko "fertility awareness method".

1. ✓Idan ruwa ruwan ya kasance mara kauri (salala) to ana kyautata zaton shine "fertile" (i.e ciki zai iya shiga kenan in Kwan ya samu sperm). Sbd a lokacin kwan zai sauka zaman jira.

2. ✓ Idan kuma ruwa ruwan ya kasance fari mai kauri to shi kuma shine "infertile" (wanda ko an sadu ciki bazai shiga ba) sbd kwan har ya riqa, karfin sa ya kare, yanzu sedai ya harziqa, se facewa.

✓To irin wannan ruwa ruwan mai kauri zaki cigaba da gani daga bayan ovulation har zuwa wani period din.

✓Daga bayan ovulation din zuwa wani period din, yawan fitowar ruwan zai na raguwa a hankali, yana zamowa mai kauri kuma mai danqo again, wani lokaci har zaki iya jinsa kamar wata gum ko glue.

✓On average dai, yana kaiwa irin kwana 11 zuwa 14. That is tsakanin ovulation dinki zuwa wani period dinki kenan.

✓Wasu lokuta kina iya ganinsa yellowish haka kafin period dinkin.

✓Idan mace taga wani irin brown discharge a bayan period dinta kuma, bayan jinin ya dauke, se ta sake ganin wani baki baki haka brown ya zo mata, to shi din yana kasance wa tsohuwar jini ne daya daskare bai samu daman fitowa ba last time. Shine yanzu yake kamo hanya.

✓Idan kuma brown discharge din kafin period ne fa? Ko kuma taga jinin Dan digo digo haka a lokacin da take tsammanin period dinta, to shi
kuma yana iya kasance wa sign ne na "implantation" daga farko farkon pregnancy. Maza se kiyi kokari kije pregnancy test domin a tabbatar da hakan ko akasin hakan. (In kin samu congratulations )

ME KE JAWO KO SANADIN FITOWAR FARIN RUWAN?

Akwai kamar category guda biyu:
1. Akwai wanda yake normal; sbd hormonal
changes.
2. Akwai kuma wanda yake abnormal: sbd infection.

1. NORMAL:

(A1).✓ yana iya kasance wa alama she ta reproductive system na mace yana functioning properly. Sbd kasance war discharge din mara kauri ne, mai yauki ne kuma mai santsi. Sannan baya wari ko qarni. Wasu suna kiran shi da "egg white mucus"

(B1). ✓Normal side effects na family planning; sakamon sauyin yanayin levels na hormones da yake jawowa, hakan yana sawa normal vaginal discharge ya karu shima.

(C1). ✓Pregnancy: wani lokaci yawan vaginal discharge kafin lokacin normal period dinki yazo yana iya zama sign ne na daukan ciki. Musamman ma idan mucus din ya kasance mai kauri kuma ruwan madara madara.

2. ABNORMAL:
(A2). ✓STIs(Sexually Transmitted Infections): kamar su Gonorhea, chylamydia, Trichomonas duk suna jawo mace tayi ta ganin fitan ruwa ta gaban ta. Gonorhea da chylamydia su yawanci basa ma nuna symptoms, sannan discharge dinsu yana nan ne yellowish haka kamar diwa diwa.

✓Shi kuma Trichomonas; discharge din da yake jawowa yana yellow ko Kore ne haka, sannan yana nuna symptoms dinsa kamar qarnin kifi kifi, kuma ga kaikayin tsiya.

(B2). ✓Candidiasis (yeast infection): shi kuma discharge dinsa fari ne mai kauri, kamar farin madara. Yawanci yafi faruwa a lokaci kafin mace taga period dinta. Yana da symptoms kamar kaikayi da jin zafi zafi a gaban mace (ta ciki da ta wajen).

(C2). ✓Bacterial Vaginosis: shima wata infection dinne da yake jawo discharge mai Kama da toka toka(gray-white) sannan yana sa warin gaba kamar qarnin kifi kifi haka.

✓ Kamar yadda kuka gani a sama tin farko, ainihin ababen da ke sa fitowar farin ruwa kenan. Da kuma yawancin lokuta da ruwa yake fito ma mata.

SHAWARA

✓Duk sanda kika ga ruwa yana fitowa ta gaban ki, kana fari ne, milk milk ne, mai kauri ne ko salala ne, mai yauki ne ko mai santsi ne, muddin baya wari kuma baya sa kaikayi ko radadi ko jin zafin gaba ko kuma yayin fitsari ko saduwa da miji, kawai ahlun salun yake fitowa abinsa, to karki tada hankali wannan normal ne. Alama she na jikin ki a matsayin ki mace, yana aiki yadda yakamata kuma cikin kocin lfyy.

✓Idan kuma kinga ruwa yana fito miki koma ya launin sa yake, kuma se tare da hakan akwai zafin gaba, kaikayin gaba, ko warin gaba, kumburin gaba, kurajen gaba ko dadewar fatar shi, ta ciki ko ta wajensa, ko kuma duka biyun, to maza maza kiyi saurin zuwa asibiti domin magani

Post a Comment

Previous Post Next Post