ZUWAN HAILA TARE DA YADDA ZAKI LURA DA KANKI

ZUWAN HAILA TARE DA YADDA ZAKI LURA DA KANKI 

HAILA, al'ada, jini, mensis ko ace period duk sunayen abu guda ne. HAILA 
wata abace da Allah ya tsara ga dukkan 'ya'yan Adam mata wadanda suka cimma wasu shekaru na rayuwa na fara aikin wasu sinadaren halittun jima'i dake jikinsu da ake kira (estrogen And progesterone) a dukkan lokaci lokaci.
Haila itace babbar alama dake nuna mace bata da juna biyu, sannan itace babbar alama dake nuna jikin mace shirye yake da ya dauki juna biyu inhar da zata sami Jima'i tsakaninta da namiji.

🧬
Su sinadaran Progesterone da Estrogen dama jariri na samun su tun aciki yayin da halittar mutum takai sati 12, amma basa fara aiki sai mace takai shekarun balaga. 

Balaga Kän bambanta wasu tun ashekara 9 suna iya fara haila don haka balagarsu kenan, wasu a shekara 11, amma da yawa sunfi farata daga shekara 13- ko -14, saide masu raunin wadannan sinadaren wasu sukan kai har shekara 17 basu fara ba koma 19. Irinsu ne saikaga ga girma da tsayi ajika amma inka kallesu babu bambanci da jikin yara wato ba fashewar kugu babu alamun fitowar nonuwa.

Haila a mafi yawa takan zo duk bayan kwana 28 kuma Sannan yawanci kwanakin basa wuce 5, saide dake Allah yai mana halittu daban-daban wasu sukan sami tazarar kwana 30 zuwa 37 sannan su kuma yin wata hailar, kuma haka jikinsu yake ba matsala bace. Wasu kuma duk bayan kwana 21.

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

Wasu sukan ga haila ta dauke musu har wata 1, 2 ko 3, toh idan mai aure ce idan haka ta faru yawanci juna biyu shine abunda muke tsammani, idan ma baki da aure kuma baki da kamun kai to kema haka muna tsammanin juna biyu ne. 

Toh amma idan duk anyi gwaji babu juna babu ko daya to sannan ake fara tunanin wasu abubuwan dakan jawo daukewarta kamar: 

☆ Idan mace tai fama da rashin lfy a tsakanin,
☆ Ko in mace ta bada gudun mawar jini,
☆ Ko macen dake shan kwayoyin bada tazara,
☆ Ko mai shan maganin larurar hawan jini,
☆ Ko Shan maganin ciwon suga,
☆ Ko sakamakon hatsari,
☆ Karancin jini
☆ Ko sa

Post a Comment

Previous Post Next Post