Barin ciki:
BARI: muna cewa barin ciki idan ciki ya zube kafin ciki yakai watanni biyar na farko (sati ashirin na farko)
Barin ciki yana zuwa da wadannan alamomin :
1- MURDAN CIKI : murdan ciki na zubewar ciki mafi yawa yana tsanani fiye da murdan ciki na al’ada.
2- CIWON BAYA: wassu lokocin ko ga wassu matan tana zuwa musu da ciwon baya mai tsanani.
3: ZUBAR JINI : sai kuma jini yabiyo baya jinin zubewar ciki yakan tsananta fiye da jinin al’ada.Kuma haka ana yawan fitar da gudajen jini.
4- Wani lokocin kawai sai aga jini ba tareda ciwon ciki ko ciwon baya ba.
Abubuwan da ake kyeutata zaton cewa shi yake kawo yawan zubewar ciki gasu :
1- MATSALAR SINADARAN HALITTAR JARIRI : wannan matslace wanda ake samu tun kafin halittar Dan Adam ana kiran sa (fatal genetic problems)
2- INFECTION: sanyin mata wanda yake sa musu Kaikayin gaba, zubewar farin Abu, ciwon mara da ciwon baya.
3- YIN AIKIN KARFI : Yin aikin karfi wanda ya wuce misali na daga cikin abubuwan sa yake kawo zubewar ciki.
4- RASHIN LAFIYA: dukkanin rashin lafiya mai zuwa da matsanancin zazzabi yakan iya haifar da matsalar zubewar ciki.
5- SHAN MAGUNGUNA: shaye shayen magunguna ba kan ka'ida ba imma na bature ko na gargajiya yana kawo zubewar ciki.
6- NAKASAR MANIYYI : samun nakasar maniyyin miji ko kwan mace yakan iya haifar da matsalar zubewar ciki.
7- MATSALAR BAKIN MAHAIFA: idan mace tana da matsalar bakin mahaifa shima cikin bazai zauna ba.
Ga wassu dalilan kuma:
- Matsalar thyroids
- Ciwon sugar
- Hawan jini
- Rashin isheshshen abinci.
- Rashi jini
- Shan sigari
Duk Lokocin da mace tasamu daya daga cikin wadannan alamomin lokocin sabon ciki:
- Ciwon ciki mai tsanani
- Ciwon baya mai tsanani
- Alamun zubda jini
Ta dakatar da :
- Aikin karfi
- Jima'i
- kada tasha ko wanne magani
- Ayi gaggawar zuwa asibity.