Matan Aure!*Matar bahaushe sau nawa kike furtawa mijinki kalmar "I LOVE YOU" da "KISSING" ɗinsa idan xai fita????

*Matan Aure!*

Matar bahaushe sau nawa kike furtawa mijinki kalmar "I LOVE YOU" da "KISSING" ɗinsa idan xai fita????

Idan mijinki ya fita aiki sau nawa kike masa text mai ƙunshe da kalaman soyayya da nuna kewarsa????

Idan mijinki ya dawo aiki shin tsalle kike ki "RUMGUME SA"tare da tarɓon sa da kalaman soyayya ko kuwa kawai kyalesa kawai kikeyi kici gaba da aikin ki????

Wai shin Idan mijinki zai fita kina tofesa da "Addu'o'IN NASARA" da feshe sa da "TURARE MAI ƘAMSHI" Da Gyara masa "HULA"ko kawai barin mijinki kike ya fita gaba-gaɗi yana warin hammata??

Idan dare yayi zaku kwanta kina sambadesa da "LABARAI" Masu daɗi ko kawai barinsa kikeyi yayi baccinsa kamar ɗan tani?????

Wai da wa 'ƴanne kaya ma kike zama a gidan mijin naki matar bahaushe???ina fatan ba zama kikeyi daga ke sai ɗaurin ƙirji  ba???

Dayawan matanmu fa idan suka haihu ɗaya biyu to zasu fara jin cewa sun tsufa tun ana saka wa miji tops da jeans da mini skirt sai a dawo ana yawo da ɗaurin ƙirji 🤦🏼‍♀️🤦🏼‍♀️🤦🏼‍♀️ shin kinsan kuwa wannan ɗaurin na batawa maza rai da ja maki raini??
  Kuma yana ɓata Nonuwa??

Yakamata matar bahaushe ki gyara alaƙarki da mijinki kisani *aure ba kashe kai bane ko kurkuku a ah aure soyayya da ƙauna ne, sai kuma haƙuri da tallafawa juna!*

Post a Comment

Previous Post Next Post