>>> ƘURJIN FARJI <<<
'Kurjin Farji wanda a turancin likita ake kira da "Bartholin cyst" wani abune kamar kurji wanda yake fitowa ta ciki kadan a farjin mace sakamakon komawar ruwa baya zuwa gaɓar da take fidda ruwa (Bartholin gland) wanda yake samarda damshi a farjin mace domin kashe kwayoyin cututtuka dake iya haifar da matsala.
Yawanci wannan kurjin baya zafi ko ƙaiƙayi saidai idan wata matsala tashafeshi zai iya fidda kuraje agefensa.
Wannar matsalar tafi shafan mata waɗanda basu tabayin aureba da wadanda sukayi haihuwa ɗaya.
>ABUBUWAN DA SUKE JAWOSHI<
1- ƙaiƙayi ko tsiron nama a farji
2- Jin ciwo a farji
3- Cutan Gonorrhea
4- Cututtukan da ake kamuwa dasu ta hanyar Jima'i
5- Cutan sanyi na infection
>> ALAMONINSA <<
1- Jin zafi lokacin saduwa, tafiya ko zama
2- kumburi awajen da yake fitowa
3- Fitan ruwa daga wajen
4- Ƙurjin ya girma yanda za'a ganshi
>> YANDA ZA'A MAGANCETA <<
1- Kidinga tsarki da ruwan ɗumi (kisa gishiri)
2- Ahaɗa man tafarnuwa da Man Habbatussauda ko Man Hulba da man Habbatussauda ko Bitter Almond oil adinga shafawa.
2- Kitafasa garin magarya da bagaruwa ko garin hulba da lalle ko ganyen gwaiba da ganyen mangworo kisa jar kanwa kadan kibarshi ya huce kidinga zama aciki.
Allah yasa adace.Everyone