Magani a gonar yaro: Magungunan cutuka 7 da Zobo ke yi ga dan Adam:
Zobo sanannen abun sha ne a duk fadin duniya kuma ana yawan amfani da shi a matsayin magani.
Zobo na da suna kala-kala a wasu sassan duniya. Ita dai launin zobo ja ne amma mai duhu.
Yana da tsami a dandano saboda hakan ne ake abun sha mai tsami da shi.
Yana da kamshi mai matukar kayatarwa.
Zobo na da matukar amfani ga lafiyar jikin dan Adam tare da zama magani ga cutuka kamar hawan jini, yawan sinadarin cholesterol, cushewar ciki, inganta garkuwar jiki da sauransu.
Zobo yana maganin cutukan hanta a dan Adam tare da rage yuwuwar kamuwa da cuta daji.
Yana inganta lafiya tare da rage kiba ga masu ita.
Yana kunshe da sinadarin Vitamin C da sauran sinadaran da ke saukar da damuwa tare da hawan jini.
Ga wasu cutuka da zobo ke magani:
1. Sauke hauhawar jini Shan zobo na sauke jini idan ya hau ga masu cutar hauhawar jini.
A wani bincike da Odigie IP suka yi a kan abubuwan da ke rage cutar hawan jini tare da bada kariya a kan ciwon zuciya, an gano zobo na kunshe da sinadaran.
2. Rage yawan Cholesterol Zobo na kunshe da sinadarin da ke rage Cholesterol, hakan na taka rawa wajen bada kariya ga cutukan zuciya tare da bude hanyoyin jini.
Zobo na da matukar amfani ga masu ciwon sukari.
Kariya daga cutukan hanta Bincike ya nuna cewa zobo na kunshe da sinadarin da ke maganin ciwukan hanta.
Duk wani matacciyar kwayar halitta mara amfani a jiki na fita bayan an sha zobo.
4. Sinadarin bada kariya daga cutar kansa Zobo na kunshe da protocatechic acid wanda ke kashe kwayar cutar kansa.
Zobo na hana girman duk wata kwayar halitta ta kansa.
5. Kashe kwayar cutar bacteria Zobo na kunshe da ascorbic acid wanda aka fi sani da Vitamin C, babban sinadarin da jiki ke bukata don inganta garkuwa daga cutuka. Ana amfani da shi wurin maganin zazzabi.
6. Maganin ciwon mara a yayin al'ada Zobo na rage ciwon mara yayin al'ada.