Da Al’umma tasan Amfanin miyar kuka ga rayuwar dan adam da mutum bazaiyi sati bai sha miyar kuka ba .
Nan Gaba Kaɗan Miyar Kukar da ake rainawa zata zama 'yar gwal kamar yadda zogale ta zama, saboda yanzu haka dai masana 'yan boko sun zurfafa bincike akan kuka, sun ce babu abun yarwa a kuka ..
Hasalima sun ce Calcium ɗin da ke cikin kuka ya nunka na Madara, da Ayaba, sun ce kuma kuka na da sinadarin protein da ake samu a nama ko kifi ko ƙwai, sannan akwai fiber a cikinta.....
Bugu da ƙari masanan sun ce kuka na ƙara garkuwar jiki, maganin hawan jini, kuma ana amfani da ita wajen maganin ciwon Oda, gina jini, maganin gajiya da sauransu....
Masanan sun ce za a iya yin shayin kuka baya ga miyan kuka da ake ci da abinci.. kuma ana so mata masu ciki su dinga sharɓar miyan kuka don yana gina 'ya'yan cikinsu.
A karshe masanan sun yiwa bishiyar kuka da kirarin bishiyar rayuwa, duba da tarin amfaninta, domin baya ga rawar da ta ke takawa ga lafiyar ɗan Adam, har da ma wajen kwalliya don tana gyara gashi ta kuma sanya fatar jiki tayi laushi da sheƙih...
Lalle kuka tayi kama da abun nan da Hausawa ke cewa da magani a gonar yaro.......
Ni daman ma abocin sharɓar miyar kuka ne, don ita ce favorite soup dina..... 'yan zu sai mu ƙara dage dantse mu bada himma, kafin 'yan boko su sa kukar ta fara yiwa talaka wahalar samu....