Shin munsan duk Abinda muke aikatawa Ubangijinmu yana kallonmu, kuma haka akwai masu rubuta aikinmu na Alkhairi ko akasin haƙa, 😭 muyi kokari muyi abinda Allah yakeso ba Abinda zuciyarmu takeso ba

Shin munsan duk Abinda muke aikatawa Ubangijinmu yana kallonmu, kuma haka akwai masu rubuta aikinmu na Alkhairi ko akasin haƙa, 😭 muyi kokari muyi abinda Allah yakeso ba Abinda zuciyarmu takeso ba 

Kuma muyi kokarin aikata Alkhairi domin aikinmu duk gidan lahira zai bimu, 

Yanzun misali idan kayi kudirin aikata wani aiki Yakamata kayi tunanin to yanzu wanan aikin da zanyi lada zan samu ko zunubi, idan lada zaka samu saika tsarkake ziciyarka kayi aikin domin Allah, idan kuma aikin zunubi zaka samu sai kayi saurin barin wannan aikin ,

Kuma idan kana abinka domin Allah babu ruwanka da Abinda wani zaice domin ba domin shi kakeyi fatanka shine samun yardar Ubangiji kuma ladanka yana wajen Allah Ta'ala,

Muna rokon Allah daya tsarkake mana zukatanmu ya daidaita dabiunmu, ya shiryamu da shiriyarsa Amin 

Allah ya tsaremu da son duniya da Rudin Duniya, da giba da munafurci, da kuma cin amana Amin 🤲

Ya Allah ka azurtamu da tuba kafin mutuwa shahada lokacin mutuwa, aljanna bayan mutuwa, bijahi Abul kasim Muhammadar Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama Amin ya ilaheee 🤲🤲

Allama Lukman Muhammad,
Allahumma salli Ala Muhammad wa Ali, 

Bisalam,

Post a Comment

Previous Post Next Post