KATAIMAKAWA YAR UWARKA MACE AKO INA TAKE.

KATAIMAKAWA YAR UWARKA MACE AKO INA TAKE.
Shin kasan halin da kanwarka take a gidan mijinta?
Ka ziyarci Yar uwarka a gidanta na Aure kuyi hira da ita kayi wasa da yaranta ka bata wani abu dai-dai iko na kyautatawa, hakan zai sa taji cewa tana da Uba na biyu mai taimakonta. 

Ka daure a yau dinnan ko naira dari biyar ne ka aika Mata dashi hakan zaisa ta farin ciki sosai, awannan yanayin da akeciki.

Ku tausayawa yan uwanku mata da suke gidan Aure ku jasu a jiki ku dinga tuntubar su akan yanayin zamansu, kuna yi musu nasiha da basu shawarwari lokaci Zuwa lokaci, hakan zai toshe wasu matsalolin gidan aure masu yawa. ALLAH YA SA MUDACE AmeenEveryone

Post a Comment

Previous Post Next Post