Shekarun Ta 23 Amma Bata Fara Al'ada (Period) Ba Ashe Namiji NeBudurwa ce yar

Shekarun Ta 23 Amma Bata Fara Al'ada (Period) Ba Ashe Namiji Ne

Budurwa ce yar shekaru 23 tazo asibitin su wani abokin aiki na, taci kwalliya tsaf tsaf har da su janbaki da tozali da jagira da ka ganta kaga yar budurwar. 
Tazo ne domin a mata hoton mara (abdominopelvic ultrasound scanning) da likita ya rubuta mata a dalilin matsalar rashin fara al'ada duk da cewa shekarunta sun kai har sun wuce lokacin da ya kamata ta fara.

Yanayin tsarin halittar mace shi ne da zaran shekarunta sun fara tasawa (ta shiga goma sha) za ta fara ganin jinin haila/al'ada sai dai daidaiku wanda basu da lafiya ko akwai matsala yanayin tsarin jikin su, wasu kuma hakanan kawai Allah ke jarabtar su.

Da aka duba hoton maran ta a computer sai aka ga bata da mahaifa (uterus) amma tana da dukkannin tsarin al'aura na namiji, ashe ba mace ba ce, namiji ne. Azzakarin shi ya shige ciki ne lokacin da aka haife shi sai su kuma su ka tsammaci mace ce, amma da a asibiti ne aka haihu ko kuma da sun kai jaririn asibiti bayan haihuwa da angaya musu cewa namiji suka haifa.

Toh yanzu namiji da yayi rayuwa a mace tun daga haihu ya zai yi daga bayan nan da aka gano namiji ne? Abin ya daure mun kai matuka. Ga shi har samari sun fara zuwa ana maganar aure. Ga shi babu nono kuma akwai 'ya'yan maraina da su ka shige ciki.

Tabbas ta/ya ban tausayi matuka. Dan Allah in an haihu a gida a dinga zuwa asibiti su dan duba lafiyar jaririn.

Wannan lamari ake cema ATYPICAL GENITALIA (AMBIGUOUS GENITALIA)

Shin a ganin ku mene ne abun yi? Everyone

Post a Comment

Previous Post Next Post