Cuttuka 10 da shuwaka ke warkarwa a jikin Dan Adam:
Ganyen Shuwaka wata ciyawa ce mai launin kore wacce ke girma a sassa daban-daban a Kasashen Nahiyar Afrika da ma Nahiyar Turai, har ya zuwa wasu yankuna na Kasashen Larabawa.
Bincike ya nuna inganci da sirrin da ke tattare da wannan ganye, kama daga ganyenta, Saiwarta, da itaciyarta.
Kabilar Igbo na amfani da ganyen su yi abinci musamman miya, su kuma Yarbawa sun Dauki Shuwaka a matsayin magani wanda suka tarar kakanninsu na amfani da ita tun asali.
A Kasar Hausa kuma, mata masu jego da masu shayarwa ne suka fi amfani da ita.
Mun yi amfani da wannan damar wajen binciko maganin da Shuwaka ke yi a jikin Dan-Adam.
Sune kamar haka:
1. Bincike ya nuna cewa ganyen Shuwaka na wanke hanta daga kwayoyin Cuta, domin hanta ta kasance abu mafi nauyi a cikin jikin Dan-Adam. ZuKar suga da kwankwadar giya da shan magungunna barkatai na illata hanta, wanda kusan duk abin da ya shafi hantar mutum to a hakika jiki zai fuskanci barazanar kamuwa da cutuka.
2. Shuwaka na taimakawa koda sosai wajen karfafa aikinta, koda wata muhimmiyar halittace da ke aikin fitar da duk wasu abubuwa marasa amfani daga cikin jiki, kamar fitsari
3. Idan kana fama da yawan tunani to sai a tace shuwaka a sanya Dan garin dabino kadan sai a zuba zuma a sha kofi daya a kowace rana, kwakwalwa za ta washe.
4. Shuwaka na maganin kasala marar misaltuwa, a nemi ganyen shuwaka a sabe a sha lita Daya da safe haka za a maimaita da yamma, a yi haka na tsawon wata Daya.
5. Idan an ci wani abinci wanda ya lalata ciki to a sha ruwan shuwaka zai taimaka wajen daidaita lamuran jikin.
6. Gudawa ga yaran da ke shan nono a saboda rikicewar nonon sai uwar ta tace shuwaka ta sha a sanda za ta kwanta, haka idan gari ya waye za ta sha.
7. Shuwaka na wanke dattin ciki.
8. Tana maganin tsutsar ciki.
9. Duk wanda ke bahaya da kyar ko mai tauri ya dinga shan ruwan shuwaka.
10. Duk mai fama da rashin bacci ya dinga shan shuwaka.