TAMBAYA DAGA MEMBER
Aslm dan Allah dakta ina da tambaya. Dan Allah idan mace ta sami wannan matsala ta zalzalowar mahaifa me ya kamata tayi. Naje asibiti kusan sau uku amman ko magani ba a bani ba.
Zazzagowar mahaifa (uterine prolapse) yanayi ne da mace takan fuskanta mai sanya mahaifarta ta rika zazzagowa har wani bangarenta ya fito ta gabanta. Yana faruwa ne sakamakon rauni (weakness) da yakan sami bango (floor) da jijiyoyi (ligaments) na mararta wadanda suke rike mahaifar. Idan ya faru, mace takan fuskanci rashin jin dadi (discomfort) da jin zafi (pains).
Abubuwa masu yawa suna kawo zazzagowar mahaifa, kamarv haka:
1. Daukar juna biyu da kuma haihuwa (pregnancy and childbirth): mafi yawancin matalar zazzagowar mahaifa tana faruwa ne saboda daukar juna biyu da kuma haihuwa. A lokacin da mace take goyon ciki, mararta tana budewa (stretching) kuma tana yin rauni (weakening). Sa’annan idan tazo yin nakudar haihuwa tana yin yunkuri wanda yake nauyayar da bangon mararta. Wadannan ayyukan sune suke sanya tsokoki da jijiyoyin mararta masu rike mahaifa su saki, don haka sai aga mahaifar tana zazzagowa bayan haihuwa.
2. Nisan shekaru (ageing): a lokacin da mace ta fara tsufa, jijiyoyin mararta wadanda ake kira “collagen” da “elastin” sukan saki, watau su rage karfi. Hakan idan ya hadu da tasirin sauye-sauyen zubar ruwan sinadarai a lokacin da daukewar al’ada (menopause) ya gabato, yana yawan hatsarin kamuwa da matsalar zazzagowar mahaifa.
3. Yin tiyata a mahaifa (uterine surgery): Idan mace ta kamu da wata rashin lafita ta mahaifa wacce ta sanya akayi mata aikin tiyata a mahaifar, to, hakan zai iya sanya bango da jiyiyoyin amahaifar suyi rauni, daga nan sai matsalar zazzagowar mahaifa ta auku.
Abubuwanda suke kara habaka hatsarin samun zazzagowar mahaifa (uterine prolapse risk factors) sune:
1. Yawan daukar juna biyu da kuma yawan haife-haife (multiple pregnancies and deliveries).
2. Haihuwar jarirai masu girma sosai (delivery of extra-large babies).
3. K