CIWON BASIR (HAEMORROID)A cikin mutane biyar mutane uku na fama da ciwon basir lokaci bayan lokaci. A yanayin sanyi Basir nayi wa wasu tsanani saboda hanyar jini yakan dan matse kadan.

CIWON BASIR (HAEMORROID)

A cikin mutane biyar mutane uku na fama da ciwon basir lokaci bayan lokaci. A yanayin sanyi Basir nayi wa wasu tsanani saboda hanyar jini yakan dan matse kadan.

A kwanakin nan an kawo mana masu basir mai tsiro wanda ta fito gaba daya taki ko mawa. Tun tana fitowa su na mayar da ita yanzu ta fito ta ki komawa tana zafi,  sun kasa zama,  sun kasa kwanciya, tsayuwar ma ba sa iyawa. 

Basir, Kumburi ne na hanyar jini a du*b*ra (anus) ta ciki ko taa waje sanadiyan nauyin ciki da ke taruwa akan wajen, yana hana jini haurawa sai hanyar jini su kumbura, su hana jini zagawa, duk wani abun da zai'iya karawa ciki dauyi(intra abdominal pressure) dai iya janyo Basir. Abubuwan sun hada da...

👉Yawan zama lokaci mai tsawo musan man a bayan gida.

👉Kiba sosai musan man mai tumbi.

👉 Rashin cin abinci mai fiber.

👉 Yawan daukan abu mai nauyi sosai.

👉 Ciki, waton juna biyu.

👉Rashin Motso jiki.

👉 Bayangida mai tauri ko zawo na lokaci mai tsawo.

👉 Rashin shan ruwa.  dss

Canza abinci da yanayin rayuwa kadai na taimakawa wajen karewa da samun lafiya.

✅ Zama cikin ruwa mai numi na mintuna goma zuwa ashirin na taimakawa sosai ga mai Basir mai tsiro,  da ta fito.

✅ Cin abinci mai fiber kamn: Fruits🍉🍍, Ganye🌿, alkama🌾, masara datsa dsss

✅ Motsa jiki akai akai.

✅ Shan ruwa.

✅ Zuwa asibiti da neman shawaran likita da wuri.

Basir har kisa nayi musanman ta ciki mai kawo zuban jini. Jinin zai ta zuba har sai an sa jini leda biyu zuwa biyar a wasu. Wani lokaci kuma ba basir din bane ya kawo hakan  don wasu  ciwoka dayawa na zuwa da hakan. Zuwa asibiti da wuri na taimakawa wanjen gano ciwon da wuri don yin magani da bada shawara.

Post a Comment

Previous Post Next Post