KARIN MAHAIFAH (FIBRIOD)MINENE FIBROID?

KARIN MAHAIFAH (FIBRIOD)

MINENE FIBROID? 

Kafin bayanin alamomin, mu fara da minene "fibroid"? Fibroid wata matsalace a mahaifar mace, wato wani yanayi ne da wani curin nama yake fitowa kuma yana girma a mahaifar mace. Ƙkululun naman mai cutar da lafiya yana ɗanfare da wani sashen mahaifar (uterus) da wasu igiyoyinsa matakam. " Fibroid" kalmar turanci ce, domin sauƙin furuci da Hausa, zamu cigaba da amfani da lafazin FAIBIROD a cikin bayanin mu anan . Anyi ƙiyasi cewa cikin mata 100, kashi 20 zuwa 50 na matan suna da fibroid, musamman a shekarunsu na samun haihuwa - wato daga shekara 16 zuwa 50. Wani ƙkiyasin kuma ya nuna cewa mata 30 zuwa 77 suna samun matsalar fibroid a lokacin shekarunsu na samun haihuwa, wato lokacin ƙkuruciyar balaga zuwa lokacin tsayawar al'adar mace saboda manyanta ko tsufanta (menopause). Mafi yawan nau'in faibirod da ake samu bayada alaka da ciwon-daji / kansa (not cancer). Ƙkululun ko ƙkwallon irin wanda baya da nasaba da ciwon-daji ne (benign/non-cancerous). Yana iya fitiwo fiye da ɗaya a mahaifa, kamar guda uku, huɗu koma fiye da haka a wurare daban-daban cikin mahifa.

ALAMOMIN MATSALAR FAIBIROD

Wasu daga cikin alamomin sun haɗa da:

1. Zubar jinin al'adah mai yawa, ko na tsawon lokaci

2. Zubar jini baaƙin lokutta ko tsakanin lokuttan haila

3. Ciwon ƙkugu, saboda ƙkululun yana danne wani sashen jiki cikin mahaifa

4. Yawan fitsari

5. Ciwon baya daga ƙkasan baya

6. Jin zafi /ciwo lokacin yin jima'i

7. Rashin jini a jika saboda yawan zubar jini

8. Rashin jin dadi a mara, musamman saboda girman ƙkululun a ciki

9. Basur maisa tsugunni a bayi saboda rashin fitar bahaya

10. Ciwon kafa 

11. Girman ciki kamar mace tana da juna biyu amma ba juna biyu bane, musamman idan faibirod din ya girma

12. Koma rashin ganin wasu ko daya daga cikin alamamomin da muka yi bayani

WASU DAGA CIKIN MATSALOLIN DA FAIBIROD ZAI IYA HADDASAWA:

- Matsala wajen haihuwa/lokacin nakuda

- Matsala yayin fama da juna biyu

- Matsalar rashin samun juna biyu / rashin ɗaukar ciki ga mace saboda ƙkululun ya toshe/taushe ko danne wani bangaren mahaifa

- Yawan bari/zubewar ciki

Yana da matukar muhimmanci mai jin daya ko fiye daga cikin wadannan matsalolin yaje asibiti domin binciki ko tana da matsalar faibirod ko akasin haka. Idan kuma kin riga kin sani to sai a nemi magani.

MINENE KE KAWO MATSALAR FAIBIROD?

Har yanzu dai masana ilimi a fannin lafiya na ƙoƙarin fahimtar cikakken dalilin daya sa ake samun fibroid. Saidai an gano cewa yawan sinadarin ESTROGEN (estarojin) a lokacin shekarun da mace ke iya samun haihuwa yana da nasaba da lokacin da mata ke samun matsalar faibirod. Daga shekara 16 zuwa 50 shine lokacin da sinadarin yafi yawa a cikin jinin mace. ESTROGEN daya ne daga cikin manyan sinadaran jikin mace, wato ESTROGEN sinadari ne na jinsin mace dake tafiyar da girman jikin mace, rayuwar mahaifarta da yanayin halittarta daya shafi jima'i . A lokacin balaga sinadarin na taimakawa yasa nonuwa da gashin mara da hammata su fito, kuma shine ke saka sha'awa ko yawan sha'awa ga mace idan yayi yawa. A lokacin balaga ƙkwayayan mahaifa (ovaries) zasu fara samar da sinadarin. Za'a iya kiran ESTROGEN da suna MAƘkERIN ƳAN MATA , domin kuwa shine ke taimakawa wajen sauye-sauyen halittar jikin mace yayinda take girma. A takaice, ESTROGEN shine sinadarin da faibirod suka dogara dashi domin samun daɗa girma a mahaifa, wato makamasin faibirod. Faibirod zai cigaba da girma har sai lokacinda mace ta bar yin al'ada saboda girma (menopause), daga nan sai ya fara ƙkanƙkancewa.

WASU DALILAI DA KA IYA SA YIWUWAR MACE TA SAMU FAIBIROD:

- Gado : Idan mahaifiyarki ko ƴyar uwarki ta taba samun fibroid zai iya yiwuwa ki samu saboda gadon jini.

- Jinsin bakar fata: Mutanen Africa ko ƙkasashen bakar fata, wato jinsin bakar fata su suka fi kowanne jinsin mata a duniya samun matsalar faibirod. Kuma matasa mata bakar fata sune suka fi samun matsalar a shekarunsu na matasa. A ƙkasashen turawa, Indiya da Chaina da sauran wasu ƙkasashen, ba kaso ake samun matansu da matsalar ba.

- Amfani da hanyoyin tsaida haihuwa (ƙkwayoyin tsaida haihuwa wani lokacin zasu iya sa faibirod ya girma), kiba ƙkarancin sindarin vitamin D, yawan cin jan-nama, rashin cin abincin ganye da yayan itatuwa, shangiya da sauransu.

Hanyoyin asibiti na magance matsalar asibiti ya ƙkunshi: aikin tiyata (surgery) domin cire ƙkululun tare da cire wani bangaren mahaifa "uterus" [Hysterectomy] wanda zai hana samun haihuwa, sa'annan wani nau'in aiki tiyatar [Myomectomy]wanda baya hana haihuwa a gaba, ƙwayoyin magani da wasu hanyoyin. Musamman idan ya girma aikin tiyata ne akafi yi domin rabuwa da matsalar.Girman faibirod na iya zama kwatankwacin girman dutse karami ko ƙkasa da haka , ko girman lemun tsami ko na zaki, ko girman ƙkwallo, girman jariri koma fiye da girman jariri, musamman idan ba'a cire shiba ko magance saba. Wasu likitocin naganin idan faibirod yakai girman inci 4 (4 inches/9-10 cm) to akwai bukatar ayi aikin tiyata domin a cire shi. Idan Kuma bai kai hakan ba insha Allahu akwai maganin da zai narkar da shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post