AMFANIN ZAITUL LAUZ ********************×*************************Zaitul Lawz (almond oil) yana da amfani mai yawa ga jikin 'DanAdam. Yana kunshe da sinadarai masu yawan gaske wadanda suketaimaka ma jikin 'Dan Adam. amma ga wasu kadan daga ciki:

AMFANIN ZAITUL LAUZ 
********************×*************************
Zaitul Lawz (almond oil) yana da amfani mai yawa ga jikin 'Dan
Adam. Yana kunshe da sinadarai masu yawan gaske wadanda suke
taimaka ma jikin 'Dan Adam. amma ga wasu kadan daga ciki:
1.Zaitul Lawz yana maganin ciwukan da suka shafi zyciyar 'Dan
Adam. domin yana kunshe da Sinadarin Folic Acid da kuma
Potassium wadanda suke mutukar taimaka ma Kuzarin zuciya.

2. Yana maganin hawan jinj, kuma yana zabgewa Cholesterol daga
jikin mutum.

3. Mutumin da yake fama da matsalar kumburin ciki ko rashin
narkewar abinci da wuri, idan yana amfani da ZAITUL LAWZ za'a
dace.

4. Mutumin da yake fama da cuta mai karya Garkuwar jiki (AIDS,
KANJAMAU) idan yana amfani da Zaitul Lawz zai samu Qarfin
jininsa zai dawo insha Allahu.

5. Idan mutum yana fama da yawan mantuwar karatu, ko kuma
rikicewar tunani, idan yayi amfani da Zaitul Lawz zai samu sauki.

6. Zaitul Lauz yana maganin tattarewar fata. Idan mutum fuskarsa
tana saurin yamushewa ko kuma alamomin tsufa sun fara
bayyana, da zarar ka fara shafa Zaitul Lawz zaka ga chanji na
mamaki. Domin kuwa shi yana maganin yankwanewar fatar jikin
Dan Adam.

7. Matan da suke fama da matsalar Karyewar gashi, idan suna
shafa Zaitul Lawz zasu samu waraka. gashinsu zai yi karfi da sheki
da laushi.

8. Zaitul Lawz yana taimaka ma jarirai wajen samun Qarfin hakora
da kuma Qashin jikinsu.

9. Zaitul Lawz yana maganin Kaikayin jiki, ciwon jiki, da sauransu
kuma yana taimaka ma gudanuwar jini ajikin Dan Adam.

10. idan mace tana sanya Zaitul Lawz acikin idanuwanta zasu
washe suyi kyau sosai.

Anan zamu tsaya da fatan Allah ya amfanar damu.

Post a Comment

Previous Post Next Post