Amfani 15 da ganyen Lansuru ke yi a jikin mutum:

Amfani 15 da ganyen Lansuru ke yi a jikin mutum:

SHARE 🔔

Ganyen lansur nada matukar mahimmanci a jikin mutum domin yana warkar da cututtuka da dama a jikin mutum.

Akan hada ganyen lansur a cikin abinci kamar shinkafa, faten dankali, faten tsaki da kuma sauran su domin taimaka wa jiki da lafiyar mutum amma wasu masanan ganyen sun ce ganyan ya fi amfani a jikin mutum idan aka ci shi danye, wato a kwada shi ko da dakakken kuli-kuli da kayan miya.

Masanan ganyen sun bayana irin amfanin da wannan ganye na lansur ke yi a jikin mutum kamar haka;
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿

1. Ganyan lansir na maganin ciwon ido: Lansuru na da sanadarin dake maganin cututtukar da ke kama ido. Cin shi na da matukar Amfani.

2. Yana maganin hawan jini.

3. Cin ganyen lansur na gyara fatar mutum. Lansuru na maganin Kyasfi dake kama fata. Ana nika shi a hada da man da ake shafawa ko kuma da ruwa a shafa a jiki. Yana gyara fata sosai.

4. Yana taimaka wa mutum cin abinci yadda ya kamata.

5. Yana maganin ciwon ciki kamar su zawo da sauransu.

6. Ganyen na kawar da ciwon zuciya.

7. Yana hana amai. Idan mutum yana yawan jin amai, lansuru na maganin shi.

8. Yana kara karfin kashi.

9. Yana kara karfin namiji.

10. Cin Ganyen lansur na kawar da warin baki.

11. Cin ganyen Lansuru na kawar da laulayin da mata kan ji idan suna jinin al’ada.

12. Yana rage kiba a jiki.

13. Yana warkar da rauni ko ciwo a jikin mutum.

14. Yana kawar da cutar siga.

15. Yana kara jini.

🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿

Post a Comment

Previous Post Next Post