KO KA SAN 'YA'YAN GWANDA NA HANA MAZA HAIHUWA ?

KO KA SAN 'YA'YAN GWANDA NA HANA MAZA HAIHUWA ?

Naga video na ta yawo a social media,a Facebook da TIKTOK akan amfanin 'ya'yan gwanda daga bakin wasu mutanen da ake yiwa kallon sun san fa'idodin tsirran itatuwa da magunna, wanda tuni wasu sun fara jarrabawa.
A cikin videon Yana nuna 'ya'yan gwanda na maganin ciwon hanta (Hepatitis).

Na Sha ganin abubuwa masu hatsarin gaske a matsayin magani a nan Facebook da sauran kafofin sada zumunta.Shi marar lafiya nema ya keyi bai san abunda keda lahani ga lafiyar shi ba.
Su Kuma wadannan masu wannan post na magunna barkatai wallahi tallahi ba karatun abun su kayi ba,da rana tsakayi aka tarbi abun a matsayin hanyar Neman kudi.Wallahi mu Ji tsoron Allah kada mu je fa rayukan mutane cikin hatsari a gobe qiyoma zamu amsa tambaya a gaban Allah.

Shi wannan 'ya'yan gwanda ana Kiran shi da papaya seeds a turance Yana matukar lahani sosai ga maniyin namiji.
Yana rage karfin maniyi waton sperm motility.
Yana rage yawan maniyin da namiji ke fitarwa zuwa low sperm count.
Idan aka dauki wata biyu zuwa uku ana Shan wannan 'ya'yan gwanda to namji zai rasa maniyi gaba daya ya koma zero count (azoospermia).
Idan aka ci gaba da Sha na fiye da wata uku to ba namiji ba alamun samun qwayoyin haihuwa waton sperm cells zai koma zero sperm count.
Ruwa kawai zai riqa fitarwa daga mazakutarsa Amma maniyi ya riga ya tafi.
Idan an ci sa'a zai iya sake dawowa zuwa bayan wani lokaci Mai tsawo,idan Bai dawo ba to shikenan namiji ya kashe kanshi gaba daya sanadin wannan maganin.
'YA'YAN gwanda family planning ne na Maza,kada a kuskura a Sha idan ba a Neman haihuwa ta katse.
Ba komai ne yake zama magani ba.
An jarraba wannan maganin ga wata karya  (dog) wacce duk bayan wata 6 tana haihuwan Yaya da yawa sai gaya har bayan shekara 3 bata Kara haihuwa ba Koda daya.
Haka Kuma an jarraba yayan gwanda ga birai su ma haihuwar su ta katse a Wani gidan dabbobi na zoo.
An jarraba 'ya'yanyan gwanda a tsakanin 6erayen gida suma haihuwar su ta tsaya.

Dan Allah mu rinka bincike kamun mu Bada fa'idar abu.
Shi ne banbancin ilmin kimiya da wannan da ba na kimiya ba,kimiya komai na magani sai sun bincika,Amma wannan ba a bincike ba a karatun side effects din abun,komai dai muka gani maganine.kowa Mai ilmin maganine,haba jama'a.

Allah ya kyauta.

Ayi shere mutane mu kula.

Post a Comment

Previous Post Next Post