Maganin Ciwon Mara Lokacin Jinin Al'ada:

 Maganin Ciwon Mara Lokacin Jinin Al'ada:



SHARE 🔔


Ciwon mara lokacin jinin al'ada, matsala ce, da ke addabar mata da yawa. Masana a wannan fanni dangane da wannan matsala ta ciwon mara yayin jinin al'ada, sun raba mata zuwa gida biyu. Kashi na farko shine, 'yan mata dake fama da ciwon mara lokacin al'ada tun kafin su yi aure. Sai wadanda ke fama da matsalar ko da bayan sun yi aure.


Dangane da kashi na farko, binciken masanan ya nuna cewa, wadansu 'yan matan su kan yi dacen rabuwa da wannan matsala da zarar sun yi aure. Amma wasu su kan ci gaba da fama da matsalar ciwon marar ko da bayan sun yi aure, wadannan sune rukuni na biyu, kuma akansu ne za mu yi bayani.


Mu na kyautata zaton mai karatu ya san cewa, jinin al'ada tsarkin mahaifa ne, abin nufi idan mace ta yi al'ada wannan ya na nuna cewa, ba komai a mahaifarta, ma'ana ba ta dauke da juna biyu ke nan. Wannan hikima ya sanya Addinin Musulunci ya lizamta wa matan dake jini yin iddar saki ta hanyar tsarki uku, wanda hakan ke tabbatar da cewa, wannan mace ba ta dauke da juna biyu. Kuma hakan sai ya tabbatar da kare nasaba, yadda ba za a dauki dan wanda ya yi saki, a kai wa wanda zai aura ba. Wannan ni'ima ce da za mu ci gaba da godewa ALLAH (S.W.T) a kan ta.


 To sai masanan su ka ce, ciwon mara a lokacin jinin haila na faruwa ne, sakamakon yadda mahaifa ke takura da kuma motsawa domin fitar da wani abu daga cikinta wanda ba shi da amfani, to hakan ne ke haifar da ciwon mara ga mata.


Kamar yadda mu ka fada a sama mata sun sha banban dangane da ciwon mara lokacin al'ada, hakanan yanayin ciwon ya sha banaban, bugu da kari dadewa da kuma lokacin da ciwon ke farawa ko ya dauke, ya banbanta daga waccan mace zuwa waccan.


Ba tare da bata lokaci ba, ga irin tsarabar da wanan shafi naku mai farin jini ya samo mu ku, yadda 'yan uwa mata za su bi, don maganin wanan matsala ta ciwon mara lokacin jinin al'ada. Mun yi kokarin kawo hanyoyi da yawa, sai ki dauki wacce ki ke ganin ta fi mi ki sauki ki jarraba, don kuwa tuni aka jarraba kowacce daga cikin hanyoyin kuma aka samu waraka da fatan Allah Ya sa mu dace, amin.


1. Amfani Da Na'a-na'a : 


Hanya ta farko da za a bi don maganin matsalar ciwon mara lokacin al'ada ita ce, ta yin amfani da na'a na'a. Anan mace, za ta juri shan na'a-na'a akai-akai. Abin nufi anan za ta ke yawan shan na'a-na'ar ne tun kafin lokacin al'adarta. Yadda za ta yi shine, za ta tafasa na'a-na'ar ta sa zuma, ko kuma zuma da madara ta ke sha akai-akai. Ba shakka wannan hadi na da fa'ida ga matan da ke fama da matsalar Ciwon mara alokacin alada.


2. Tsamiya Da Gauta.


Shi ma wannna wani hadi ne da aka jarraba kuma aka ga amfaninsa. Yadda mace za ta yi shine, ta samu tsamiyarta, amma tsohuwa, sai ta jika ta da ruwa, ta jefa bushashiyar gauta a ciki ta ke shan ruwan kwana biyu kafin zuwan jinin hailarta, har lokacin da hailar zata fara zuwa. 


3. Albabunaj.


Albabunaj na da matukar tasiri wajen magance ciwon mara ga mata lokacin jinin al'ada. Kuma amfani da shi na da sauki ainun. Yadda mace za ta yi shine, za ta tafasawa shi a ruwa ne, ta ke sha. Za ta iya shan sa zalla ba tare da ta sanya komai cikinsa ba, ko kuma idan ta so ta ke zuba zuma mai kayau marar hadi ta ke sha. Mata da yawa sun gwada wannan hadi kuma sun dace kan matsalar ciwon mara lokacin al'ada.


4. Kustul Hindi.


Wannan wani hadi ne mai matukar fa'ida kan matsalar ciwon mara lokacin al'ada ta mata. Kamar hadin da muka bayar mai lamba na 3 da ke sama, shi ma wanan wani hadi ne mai saukin hadawa kwarai da gaske. Za ki samu Kustul Hindinki ki jika shi a ruwa ki ke sha sau byu a yini, wato, safe da yamma shima. Hakika ya na magance matsalar ciwon mara ko rashin zuwan jinin sosai, ko kuma rikicewar jinin al'adar.


5. Hadin Habbatus Saudah.


Yadda za ki yi wannan hadi shine, ki samo garin habbatus sauda da garin hulba da kuma garin kusdul hindi ( kowannensu cikin karamin cokali daya) sai ki tafasa su a waje guda, sanan ki tace, daga nan sai ki samu zumar ki mai kyau wacce ba ta da mis ki hada da Khal tuffa cokali uku ki ke sha. Wannan ma hadi ne da aka jarrba kuma ya na da kyau matuka. 


6. Kirfa (Cinnoma).


Za ki samu, Kirfa (Cinnamon) ki dinga tafasawa ki na sha, ta na maganin Ciwon mara alokacin alada. Kuma mujarrabi ne.

Karanta: Matsalar Saurin Inzali Da Hanyoyin Magance Ta.


7. Man Zaitun. 


Shi kuma yadda za a yi shine, a Karanta ayoyin Alqur'ani a tofa cikinsa sannan Mace ta rika shan cokali guda safe da yamma kullum har zuwa lokacin zuwan Jinin al'adarta. Kuma zata rika shafawa ajikinta har Mararta (Amma banda al'aurarta). Shi ma wannan hadin an gwada shi kuma an dace.


FADAKARWA: Wadannan hanyoyi da shafin ya kawo don magance matsalar ciwon mara lokacin jinin al'ada, mun kawo ne don taimakawa 'yan uwa mata, kuma kamar yadda mu ka zayyana a sama, an gwada wadannan hanyoyi kuma an samu waraka. Sai dai shawara anan ita ce, ga 'yar uwar da ta jarraba amma ba ta dace ba, sai ta tuntubi Likita ma fi kusa da ita. ALLAH YA sa mu dace, amin.

Post a Comment

Previous Post Next Post