Yadda Za A Rabu Da Gishirin Fuska Har Abada Da Yardar Allah
Shin mene ne gishirin fuska? Gishirin fuska dai ana kiransa da white heads da Ingilishi.
Abubuwan da ke kawo shi, shi ne yawan gumi a fuska ko maikon fuska.
Idan muka yi gumi, fuskarmu takan fitar da maiko. Idan ba mu damu da wanke fuskarmu a lokacin da ta yi gumi ba, to hakan yakan taru ne ya zama gishirin fuska.
Yana nan fari a kan fuska. Idan ko muka yi kokarinarin cire gishirin fuskar da hannu, hakan kan janyo kurajen fuska.
Saboda haka ne na kawo mana hanyoyi da dama da za mu bi don rabuwa da gishirin fuska.
• A rika wanke fuska akalla sau biyu a rana da ruwan dumi da sabulu. Yin haka na rage fesowar gishirin fuska. Kuma yakan hana su fitowa.
• A zuba tafasasshen ruwa a kwano ko roba. Sannan mu rufe kanmu da tawul sai mu sanya kanmu a saman ruwan
zafin domin fuskar ta tiraru na tsawon minti 10. Yin haka na narkar da maikon fuskar (gishirin fuska).
Karanta Wannan: Yadda Ake Hadin Dauwamammiyar Ni'ima
• A samu baking soda. Za mu iya samunsa a shagon da ake sayar da kayan kek sai mu kwaba a ruwa sannan mu shafa a fuskarmu. Bayan haka, sai mu jira ya bushe. Idan ya bushe, sai mu wanke da ruwan dumi.
• Idan kuma ba za mu iya tirara fuskar ba, zamu iya sanya tawul a ruwan zafi, sannan mu matse kafin mu kai fuskarmu.
• Shan ruwa kamar kofi 8 ko 10 a rana na wanke maikon fuska kuma yana hana fitowar gishirin fuska.
• Lemun tsami na bushar da maikon fuska. Za mu iya shafa ruwan lemun tsami a auduga sannan mu goge fuskarmu da shi. Hakan na rage gishirin fuska.
• Zuma na taimakawa wajen rage gishirin fuska da kurajen fuska. Mu
shafa zuma a fuskarmu. Sai mu bar ta na tsawon minti 10. Sannan mu wanke da ruwan dumi.
Idan muna son rabuwa da irin wadannan kuraje na fuska da kuma gishirin fuska, amfani da hadin gargajiya irin namu na saurin warkar da cututtukan fata.
Za mu iya amfani da daya daga cikin wadanda na lissafo don magance gishirin fuska.