Alkaki

ALKAKI


INGREDIENTS:
1. Alkama mudu ďaya
2. Sugar gwangwani 6
3. Nono na shanu 
4. Man shanu ďanye 
5. Butter simas rabi
6. Mai kwalba biyu

A sheqe alkama a cire dukkan dattin ko a wanke a baza shi a rana ya bushe. Sai a kai babban inji a mishi 'barjin fate idan aka dawo dashi a bude tsakiyar alkaman a kwanon kwabi a juye nonon shanu, butter, man shanu, sai a murje shi da kyau ya hade. Sai a zuba ruwa amma kwabi zaki mishi mai qarfin gaske yanda zai hade da kyar, Sai a rufe shi ya kwana.

Idan kika tashi da safe sai ki jiqa kanwa, ki rinqa yayyafa masa kina hadashi kina bugawa. Har sai kin diba a hannun ki kin masa naďin alkaki kin ga bai karye ba. Wato kin yi tsaho dashi kin murza duka bai karye ba. Kin ga ba qaramin bugu zaki masa ba. Ba a jibga masa ruwa sam, yayyafa masa zaki rinqa yi kina buga shi.
Sai a zuba sugar a tukunya, a zuba ruwa kamar kofi uku a ďaura a wuta. Idan mai buqatar sugar alkakin ya rinqa ďiga ne bayan ya gama shiga cikin sa sai ki saka tsamiya kwaya đaya ko table spoon na lemun tsami yayin da kike dafawa. In kuma kina son ya bushe a jikin sa kamar nawa to kada kisa.

Wurin dafa sugar a kula yana fara yin kumfar farko na dahuwa a ďiba a cokali yana ďan fara shan iska

Post a Comment

Previous Post Next Post