Alkubus

**ALKUBUS**

**Masha Allah**
Gamu tafe da alkubus

Kayan haɗi* 

Filawa kwata 1/4
Gishiri karamin cokali 1
Man gyada badayawaba
Yeast na 50
baking powder rabin cokali
Sukari rabin cokali

Acikin mazubinki ki tankaɗe flour ki kizuba sukari,man gyaɗa, gishiri,baking powder, dakuma yeast ɗinki,ki motsa har su hade jikinsu, sannan sekisa ruwa madaidaici kijujjuya kar yayi ruwa kamar dai yanda nagwada maku a hotuna 
Sekiyita bukagashi dan yayi kyau sosai idan kuma kikasa kyuwa ke kika sani 🤣  idan kika gama seki saka a rana ki rufe shi har ya tashi,seki dauko gwangwanayenki kishafa masu mai seki zuzzuba kullun karfa kicika kisa kar yakai rabi dan idan yayi yawa ze iya zuba, seki barshi na kamar tsawon minti 20 zuwa 30 zakiga yadan ƙara tashi shikenan seki jera a tukunya ki turara
Bayan wani lokaci seki dauko 1 kiɓara kiga idan har babu tuwo tsaka to ya dahu seki sauke yahuce kicire shi daga gwangwanayen idan kuma kikayi garaje kika ƙone matsalarkice 🙄

Shikenan se ci 😋😋

Note;
Zaki iya sa rariyar karfe kafin kisa murfin tukunya wanda zakisa daga kasa yadda ruwan bareyi saurin ƙarewaba 
Idan yeast yadaɗe baya tashi kuma ruwan zafi na kashe kwayoyin yeast yahanashi tashi sbd hk idan kina bukata zaki iyasa riwan ɗumi ba ruwan zafi ba
Kuma abinda yasa akesaka sukari sbd yayi saƙa me kyau

Idan kinyi daidai zakiga daidai ☑️
Idan bakiyi dai daiba ❎
Ke kika sani 🤣🤣

Se mun haɗe 💃💃😘

Post a Comment

Previous Post Next Post