*CABBAGE SAUCE golden KITCHENπ¨πΎπ³π©πΎπ³ππππ²π₯£*
Abubuwan buqataππΎ
Cabbage
Tattasai
Attarugu
Albasa
Sinadarin dandano (Maggi)
Gishiri
Curry
Mai
Tafarnuwa
Citta
Akwai Hanyoyi guda2 da ake bi domin wanke cabbage.
ππΎZaki iya yanka cabbage naki kafin wanke shi ,kasancewar shi bayada datti a jikinsa kamar kasar,sai dai ruwa zai iya Yi wa miyar yawa bayan an zuba cabbage din a miyar.
ππΎZa kuma ki iya wanke cabbage naki a gudan sa,kafin ki yanka shi. Hakan zai sanya ba zai Tara ruwa a jikinsa ba balle bayan kin zuba shi a miyar,ya sanya miyar tayi ruwa sosai.
Ya danganta da wane Kika Fi buqata,sai kiyi amfani da ita.
*YANDA ZAKI HADA MIYAR CABBAGE*
Zaki yanka cabbage naki yanda kike buqatan girman yankansa ki ajiye a kwando a gefe daya. Ki wanke attarugu,tattasai,albasa,citta da tafarnuwa ki jajjaga ki ajiye...
Zaki saka mai da yar albasa a kan wuta ki soya na 1min sai ki zuba jajjagen aciki ki soya kamar na 10mins,kafin ki saka sinadarin dandano,gishiri,curry ki juya Sai ki rife ta Dan kara dahuwa ko na 10mins Sai ki kawo yankakken cabbage naki ki zuba akai ki juya su hade jikinsu.sai ki rage wuta domin cabbage din ya Dan risina,sai ki sauke shikenan kin kammala.
Tags:
food