lemon Ardeb

LEMON ARDEB

Assalamu alaikum. Uwargida, tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya.

Na san mutane da dama ba su san me ake kira ‘ardeb’ ba. Wannan ardeb dai yana nan ne kamar lemun tsamiya. Kuma yana da alaka da mutanen Maiduguri.

A irin wannan yanayi da muka shiga ana yawan hada wannan ‘ardeb’ din ko kuma jus din tsamiya, sannan a sanya shi ya yi sanyi domin sanyaya zuciya a lokacin zafi. Akwai hanyoyi biyu da ake bi don yin wannan hadin.

A sha karatu lafiya

 

KAYAN HADI

Tsamiya
Siga 
Masoro 
Kanamfari 
Citta 
Ruwa 
A samu tsamiya a wanke tsaf ya fita sannan a jikata ta jiku sannan a daka kayan yaji; masoro da citta da kuma kanamfari. Sannan a dora tukunya a wuta, bayan tayi zafi, sannan a zuba sukari, har sai ya narke, sannan a zuba ruwa. A dauko wannan jikakkiyar tsamiyar a tace a zuba a cikin ruwan sukarin, sannan a tankade dakakken kayan yajin a zuba a gauraya sannan; Kuma sanya shi a gidan sanyi domin dandano ya fito sosai.

Post a Comment

Previous Post Next Post