Uwar Gida idan babu ke babu cikkane gida haka zalika rashinki tamkar rashin wani bangarene na jiki, Assalamu Alaikum barkanmu da war haka barkanmu da sake saduwa daku A cikin shirin namu na Girke-Girke wadda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha.
A makonin da su ka gaba mun kawo muku saloli daban daban na yadda ake hada abincin zamani haka zalika yau mun kawo muku wata sabuwar hanya ta yadda ake hada soyayyar taliya da kaza cikin sauki.
Soyayyar Taliya Da kaza
Kowace mace tana da irin nata dabarun wajen sarrafa girki haka zalika ko wace mace da yadda abincin ta ke dandano ko daya ke wasu lokutan ya dan gana da ababen da akayi amfani dasu wajen hada girkin.
Yana da kyau mata su rika canza yanayin yadda suke sarrafa girki domin shi harshe a kullum yana son dandano daban-daban. Yana da kyau mace a kullum ta kasance kwararriya a wajen sarrafa girki ta bangarori daban-daban domin yin hakan yakan kara dankon soyayya da kuma kauna daga shi mai gida haka zalika ta wajen yara.
Duk yadda kike da kyau, komin yadda kike nunawa mai gida kauna idan har baki iya girki da zai motsa kunnuwansa ba to wasu lokutan zai iya tsinci kansa a duniyar rashin kaunarki wadda zai iya kaiwa da ya nuna miki Zahiri.
Domin girka Soyayyar Taliya da Kaza ga ababen da ake bukata kamar haka:
Taliya
Tumatir
Nama
Kaza
Karas
Koren wake
‘peas’
Magi
Kori
Tafarnuwa
Citta da kuma
Albasa
Matakan Da za’abi wajen hadawa:
Da fari za’a yayyankan albasa da tumatiri a aje a gefe guda sannan a dora ruwa kan wuta, bayan ya tafasa sosai sai a zuba taliya da gishiri kadan a lokaci guda cikin ruwan. Idan taliyar ta yi tafasa daya sai a tsame a ajiye a gefe guda. Sannan adora man gyada a wuta bayan ya soyu sai a zuba yankakkiyar albasa da yankakken tumatir da jajjagaggen attarugu a ciki.
A tafasa nama, a tsamesa daga cikin ruwa sannan a yayyanka shi kanana sai a zuba. A zuba magi, kori da garin tafarnuwa da citta sannan a dauko wannan taliyar a zuba ta a ciki a gauraya. A zuba ruwa kadan sannan a rufe bayan mintuna biyar zuwa takwas sai a sauke daga wuta.
Abu na gaba da za’ayi anan shine a tafasa kaza ta yi laushi hade da magi da kayan kanshi sannan a soya da man gyada. A soya tumatir da attarugu da albasa. A zuba magi da citta da tafarnuwa. Bayan an tabbatar sun soyu sannan a dauko kazan a cakuda shi a ciki sannan a dora a kan wannan soyayyar taliyar.
Soyayyar Taliya Da kaza
Tags:
food