fried peppers potatoes

*FRIED PEPPER POTATOES🍠🫑 BY gloden KITCHEN👨🏾‍🍳👩🏾‍🍳🍝🍛🍲🥣🍜*

Abubuwan buqata👇🏾
Potatoes🍠
Attarugu
Tattasai
Albasa
Curry
Sinadarin dandano(seasonings)
Mai
Citta
Tafarnuwa
Spices
Da farko zaki samu dankalin ki (ya danganta da wane kalan dankali kike da shi,ni dai nayi amfani da Dankalin Hausa da kuma Dankalin turawa (wato irish) dik a guri daya,nayi hakan ne saboda na nuna maku cewar zaku iya hadesu guri daya yayin yin wannan kalan soyen ko kuma kiyi amfani da kowanne daban) bayan kin fere kin wanke Sai ki tafasa su (tafasa daya ya wadatar Musamman idan sabon dankali ne) na soya su a ruwan mai (na soma soya irish kafin na soya na Hausan saboda na daidaita soyuwarsu) bayan na siya Sai na jajjaga attarugu da tattasai,citta da tafarnuwa,a gefe daya na Dora pan a kan wuta tare da man gyada Sai na juye jajjagen akai na soya,na saka sinadarin dandano,curry,gishiri kadan na soya,sai na juye dankalin tare da albasa akai na juya suka hade jikinsu,kafin na Dan saka ruwa kadan na juya na rife for some minutes Sai na kwashe. Sai kuma na fasa kwai a wani mazubi daban,na saka jajjagen attarugu,na yanka masa albasa akai,na saka Maggi na kade na toya wainar kwai na Dora a saman dankalin.. Shikenan na kammala Sai serving.


Post a Comment

Previous Post Next Post