Addu,a Mai kyau ga ma,arata

KI ISAR DASHI ZUWA GA KOWACE ME AURE SABODA TA YI WA MIJINTA ADDU'A, KI JIRA LADARKI KUMA GA ALLAH.

ADDU'A MAI KYAU GA MA'AURATA.

Ya Ubangiji Mai Mulki da Mallaka Ka mallakamin wanda kamallaka masa lamarina,🤲🏼
Ya Allah kashiryaminshi ka maidashi farincikin idanuna, kar kuma yaga wata idan ba niba,
Ya Allah ka gyara tsakaninmu kar kasa fushinka a tsakaninmu Ka saka fushinka akan maqiyinka dakuma maqiyinmu.🤲🏼

Allah ka boye masa aybina kuma ka boyemin aybinshi, Kuma ka bayana masa kyawawan abubuwana nima ka bayyana mani nashi,
Kuma kabani yarda da abinda karubutamin ka kuma sakamin albarka aciki,🤲🏼

Allah ka azurtani da soyayarshi da yardanshi da kuma gaskiyan zancenshi, In kuma yayi fushi ka jefi bakinshi da kalman La ilaha ilallah, kakuma kwantarda fushinshi da lahaula wala quwata illa billah,🤲🏼

Ya Allah ka azurtani da tausayin mijina da ya'ya'na dakuma kudi halal da kuma karatun Alqur'aani har abada,🤲🏼

Ya Allah Ka daidaita tsakanin kowace mace da mijinta, kuma Ka sa qauna babba a tsakaninsu kakuma kore hasada a tsakaninsu, masoya akowane lokaci kowane miji yadinga kallon matarsa da gani mafi kyau, Ka kuma qara ladansu Ka yafemusu kayimusu rahama.🤲🏼

( KIYADA DAN MALAIKU ZASUCE MIKI KEMA ALLAH YAMIKI IRINSHI ).

KU ISAR DASHI GA MA AURATA

#SheikhImamAbubakarBalaGana (Hafizahullah)

Post a Comment

Previous Post Next Post