[4/13, 9:46 AM] +234 813 420 3941: *SALLAR IDI.*
HIKIMAR SHAR’ANTA TA.
Sallar idi na daga cikin alamomin addinin musulunci bayyanannu wadda Allah ya kebance alummar Annabi Muhammad ﷺ da su, wajan tabbatar da godiya ga Allah majibanci akan kammala azumi watan Ramadan (A karamar sallah kenan), da kuma ziyartar dakin Allah mai alfarma (A babbar sallah kenan), kamar yadda ya kasance a idi, akwai kira zuwa ga tausayi da jinkai tsakanin al’ummar musulmi da haduwarsu a wuri daya, da kuma daidaita zukata.
[4/13, 9:48 AM] +234 813 420 3941: *HUKUNCINTA.*
Sallar idi farilla ce ta kifaya, Manzon Allah ﷺ da Halifofi na bayan sa sun kasance suna aikata ta, kuma sunnah ce mai karfi akan kowanne musulmi na miji ko mace, kuma an shar’anta ta ga mazauna banda matafiya.
[4/13, 9:49 AM] +234 813 420 3941: *SHARUDDAN TA.*
Shurudanta kamar juma’ah ce, saidai banda kutuba hudubobi biyu, domin su sunna ne a sallar idi, kuma ana yin su ne bayan sallah, (ita kuma juma’a kafin sallah).
*LOKACINTA.*
Daga dagowar rana da safe gwargwadon tsawon mashi, har zuwa zawali (wato gushewar rana daga tsakiya). Idan ba’a san da idi ba har bayan zawali sai a sallace ta gobe a matsayin ranko na lokacin ta *YADDA AKE SALLAR IDI.*
Sallar idi raka’a biyu ce, domin fadin Sayyidina Umar t: “Sallar Fitri (wato karamar sallah) da Adha (babbar sallah) raka’o’i biyu ne cikakku ba tare da ragi ba, a kan harshen Annabin ku ﷺ, duk wanda ya kirkiro to ya tabe”. {Ahmad}.
Ana sallar idi ne kafin kutuba, za’a yi kabbara a raka’ar farko bayan kabbarar harama, kuma kafin ta’aewuzi kabba rori shida, a raka’a ta biyu kuma za’a yi kabbara kafin karatu sau biyar.
[4/13, 9:58 AM] +234 813 420 3941: *WURIN DA AKE YIN SALLAR.*
Ana sallar idi a fili ne. Kuma ya halasta ayi ta a masllaci idan bukata ta kama.
*SUNNONIN SALLAR IDI.*
An sunnanta yin kabarbari ba tare da kayyade cewa sai bayan idar da salloliba, da kuma bayyanar da kabarbarin tun a daren sallah din
An so a gabatar da ita a babbar sallah da wuri, kuma a jinkirta ta a karamar sallah.
An sunnanta cin abinci kafin a fita a karamar sallah, kodai dabino dabino, da kuma kame baki daga barin cin abinci a lokacin babbar sallah, domin a ci daga abin da aka yanka.