Ba duk mata bane suke iya fitowa fili su nunawa namiji suna sonsa ba.

Ga Yadda Zaki Nunawa Namiji Kina Sonsa Cikin Dabaru:


Ba duk mata bane suke iya fitowa fili su nunawa namiji suna sonsa ba. Wasu ko dai saboda kunya wasu kuwa suna gudun gori irina wawayen maza.

Ga wasu dabaru cikin sauki na zaki haskawa namiji kina ra'ayin sa. Kaman yadda muka kawo wasu darusan irinsu a baya.
Idan kina son nunawa namiji kina sonsa ba tare da kin furta ba. Kiyi kokarin ako yaushe kina son kusantar sa ko ta zahiri ko ta hanyar kiran waya.

Yi kokarin neman sanin halin da yake duk bayan kwana biyu ko da ba shi ya nemeki ba.

Wani hanyar nunawa namiji kina sonsa cikin dabara shine neman taimako ko shawaransa.

Kina iya neman taimakonsa akan wani abunda ba fin karfi ki yayi ba. Koda bude miki lemun kwalba ne. Ko rakiya.

Haka nan ki kirkiro wata maganar da zaki nuna masa shawararsa kawai kike nema game da abun. Idan Namiji mai fahimta ne basai kin yi hakan sama da sau biyu ba shima zai dau haske.

Gayyace shi wani abunki na musamman. Idan kina bukin ranar Haihuwar ki, ko daurin auren wani naki. Kina iya gayya tarsa kuma ki nuna masa mahimmancin sa a wajen taron.

Kiyi kokarin yin kusanci dashi ba tare da kinyi yadda zaki gundureshi ba. Kada ya zama a kullum sai kin ce dole kinyi magana da shi. Amma kuma kada ki dau lokaci mai tsawo kina jan aji.

Ki kula, shi soyayya kaman yadda yake shiga farat daya, haka nan yana shigar mutum a hankali musamman mutumin da kake kusantar sa. Don haka kada ki damu na cewa da kin soma yi masa kyerkera zai iya fadawa, ci gaba da yi masa hakan cikin hakuri lokacin da ya kamu shine zai juwo miki.

Post a Comment

Previous Post Next Post