𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑 Ƙ𝐀𝐑𝐙𝐔𝐖𝐀 𝐖𝐀𝐓𝐎 [𝐒𝐂𝐀𝐁𝐈𝐄𝐒] 𝐀 𝐓𝐔𝐑𝐀𝐍𝐂𝐄~~~~~~~~▪︎●●•◇•●●▪︎~~~~

𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑 Ƙ𝐀𝐑𝐙𝐔𝐖𝐀 𝐖𝐀𝐓𝐎 [𝐒𝐂𝐀𝐁𝐈𝐄𝐒] 𝐀 𝐓𝐔𝐑𝐀𝐍𝐂𝐄
~~~~~~~~▪︎●●•◇•●●▪︎~~~~~~~~

Ƙarzuwa wacce wasu kan kira da “lagwada" larura ce dake shafar fatar jiki sanadiyar kwaso wata ƙ𝐰𝐚𝐫𝐤𝐰𝐚𝐭𝐚 me suna "𝒔𝒂𝒌𝒐𝒇𝒕𝒊 𝒔𝒊𝒌𝒂𝒃𝒊" wanda wannan ƙwarkwata ana iya samunta ajikin dabbobin da ake kira 𝐌𝐚𝐦𝐦𝐚𝐥𝐬; wato dabbobi masu Nono, gashi ajika, da kuma ƙashin gadon baya. Irinsu Maguna, karnuka, Awakai, jemagu, tumaki, dawakai, shanu, dama mutane baki daya. 

Ita wannan ƙ𝐰𝐚𝐫𝐤𝐰𝐚𝐭𝐚 kamar yadda kuke ganin hotonta akasa, ido bai iya ganinta kuru-kuru saide in ansa na'urar kara karfin gani. Wannan tasa inta hau jikin mutum takan yi rami, ta kwanta a bisa fata, batare da ya sani ba, tai 𝐤𝐰𝐚𝐢🥚 wanda idan kwan yakai ga lokacin 𝐤𝐲𝐚𝐧𝐤𝐲𝐚𝐬𝐡𝐞𝐰𝐚, sai su fito daga nan kuma sai su yadu gurare daban-daban sui wasu sababbin ramuka afatar duk batare da mutum yasani ba.

Su wadannan sabbin ƙwarkwatar da aka kyankyashe ke samar da kuraje a wurare daban daban da suka watsu na fatar jikin mutum.

Wani abu kuma shine su kurajen da kwarkwatar ke sawa suna da matukar kaikayi, hakan kesa wanda ya kamu da cutar ya rika yin soshe-soshe daga lokaci zuwa lokaci.

~~~~~~~~▪︎●●•◇•●●▪︎~~~~~~~~

𝐒𝐔𝐖𝐀 𝐊𝐀𝐍 𝐊𝐀𝐌𝐔 𝐃𝐀 𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑

Ita wannan larura kowa na iya kamuwa da ita, saide tafi damun yara, cutar karzuwa tana shafar Maza da Mata. Kwayayen cutar kan dau sati 1 zuwa 5 kafin cutar ta bayyana.

Saide idan cutar ta bayyana jikin wani har kuraje da ruwayen ciwon suka bayyana toh a irin wannan lokaci duk wanda ya shafa zai iya kamuwa nan da nan sannan alamun cutar na iya fara bayyana cikin ‘yan kwanaki, batare da daukar satuttuka ba, domin shi ba kwayeyen cutar bane kadai ya kwasa hadda ruwan gubar kwarkwatar tare da ita kanta. 

Anan zamu fahimci daga yadda cutar ke samuwa, zuba kwayaye ta yadu zuwa cikin jiki zaku fahimci kazanta ce 𝐭𝐮𝐬𝐡𝐞𝐧 𝐥𝐚𝐫𝐮𝐫𝐚𝐫, domin in mutum na lura da tsaftar jiki da tufafi akai-akai ba ta yadda kwarkwatar zata sami gurbi.

~~~~~~~~▪︎●●•◇•●●▪︎~~~~~~~~

𝐀𝐋𝐀𝐌𝐎𝐌𝐈𝐍 𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑 𝐊𝐀𝐑𝐙𝐔𝐖𝐀

Babban abinda ke damun wanda ya kamu da ita shine yadda jikinsa zaita damun shi da kaikayi, wanda yawanci wannan yafi faruwa da dare, ko kuma bayan yayi wanka da ruwan zafi. 

Haka ma akwai jin kaikayi da ganin kuraje masu ruwa a duwawu, tsakanin ‘yan yatsu, damtse, kafada, da kuma idon kafa da kuma karkashin Nono wajen Mata. 

Hakama ana iya ganinsu a wuraren da ya haďa da jakar maraina da kuma azzakari ajikin Maza. 

𝘼𝙗𝙪𝙣𝙙𝙖 𝙠𝙚 𝙗𝙞𝙮𝙤 𝙗𝙖𝙮𝙖𝙣 𝙠𝙪𝙧𝙖𝙟𝙚𝙣:

Sakamakon kurajen da kwayar cutar ta haddasa ajika sosawar da me ciwon keyi domin samun saukin kaikayin kansa kansu ya huje inda hakan ke ba kwayar cuta musamman dangin bakteriya damar hawa kansu.

Hawan kwayoyin cutar kuma na jawo bayyanar kaluluwa tare da jin sassandarewar guiwoyi duba da yadda bai iya mikewa ya tafi sak in cutar ta shafi duwawu.

Haka sakamakon kurajen, in mutum ya kwanta bacci da safe na iya farkowa yaji kayansa duk sun manne masa ajika, saboda ruwan nada danqo sosai.

~~~~~~~~▪︎●●•◇•●●▪︎~~~~~~~~

𝐇𝐀𝐍𝐘𝐎𝐘𝐈𝐍 𝐊𝐀𝐌𝐔𝐖𝐀 𝐃𝐀 𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑

■- Ana iya daukar ita cutar ta hanyar saduwa tsakanin mace da namiji, wato idan jiki ya hadu da jiki.

■- Haka amfani da kayayyakin wanda ke dauke da cutar kamar amfani da; riga, wando ko tawul 

■- Haka ma ta hanyar kwanciya bisa gado ko katifar wanda ya kamu da cutar ko inda me cutar ya kwanta yabar jurwayen ruwan ciwon.

■- Haka yiwa yara wanka da soson wanka guda, ko sakasu robar wanka guda na iya sa wadanda basu kamu bama su kamu.

■- Sai kuma shiga cunkoson mutane yana daga cikin muhimmin abunda kesa akamu da cutar, kamar kasuwa, makarantun kwana da sauransu, saboda wani bakasan meke jikinsa. Hakama cunkoson yara wajen kwanciya.

■- Sannan cutar na iya yaduwa ta shafi mutane da yawa a irin gidajen Kurkuku, gidan marayu, ko kuma wuraren da aka tsugunnar da mutane (camp), da kuma Barrack kamar ta ‘yan sanda ko sojoji duk wadannan wuraren cutar tana iya yin yaduwar da ba'a zata ba.

■- Haka ma karancin tsafta aguraren saukar baki wato hotels hotels... saboda akan sami karancin tsafta a wasu hotels din, musamman idan suka ga bqbu datti kakka6e gurin suke kurum afeshesa. Don haka sai ana lura.

■- Cutar ma ana iya kamuwa da ita aguraren kula da marasa lafiya idan gadajen ko shimfidar gadajen ba'a tsaftace su da kyau.
 
𝐇𝐚𝐤𝐚 𝐦𝐚:

Samun wurin zama mai ni’ima ga kwarkwatar ka iya taimaka mata ta cigaba da rayuwa koda kuwa zata yi kana uku ne ba bisa fatar jikin mutum ba.

~~~~~~~~▪︎●●•◇•●●▪︎~~~~~~~~

𝐌𝐄𝐍𝐄𝐍𝐄 𝐑𝐈𝐆𝐀𝐊𝐀𝐅𝐈𝐍 𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑 

Rigakafi shine tsaftar jiki, makwanci da ta kayan sawa.

𝐘𝐀 𝐓𝐒𝐀𝐅𝐓𝐀𝐑 𝐙𝐀𝐓𝐀 𝐊𝐀𝐒𝐀𝐍𝐂𝐄

Za'a tsaftace jiki ta hanyar wanka da wanki, yanke farcen hanaye da kafafuwa, aske gashin kai ga maza ko kitso a mata, goge hakora idan antashi daga barci kafin aci abinci ko bayan anci abinci.

𝐌𝐄𝐍𝐄𝐍𝐄 𝐈𝐋𝐋𝐀𝐑 𝐊𝐀𝐑𝐀𝐍𝐂𝐈𝐍 𝐓𝐒𝐀𝐅𝐓𝐀𝐑

Karancin tsafta ko a addinance ba abune me kyau ba, Shike taimakawa yaduwar cututtuka tare da karin munanarsu, gami da haifar da warin jiki tare da kawo kyamata daga cikin mutane. Kai karancin tsafta na qarawa mutum kusanci da mutuwar wuri.

~~~~~~~~▪︎●●•◇•●●▪︎~~~~~~~~

𝐌𝐀𝐆𝐀𝐍𝐈𝐍 𝐖𝐀𝐍𝐍𝐀𝐍 𝐂𝐔𝐓𝐀 𝐓𝐀 𝐊𝐀𝐑𝐙𝐔𝐖𝐀

Maganin wannan cutar sai anje ga likita, saboda ainishin cutar kunga kwarone wato protozoal infection, maganin cutar shine rukunin magunguna 𝑨𝒏𝒕𝒊-𝑷𝒂𝒓𝒂𝒔𝒊𝒕𝒊𝒄, to amma kuma illolin da kwarkwatar keyi na huda fata, ruwa, baroro, kaikayi ba'a rasa bakteriya don haka nan ma sai anhada da magunguna rukunin 𝑨𝒏𝒕𝒊-𝒃𝒊𝒐𝒕𝒊𝒄𝒔. 

Sannan kaikayin da fashewar fatar nasa aqarawa mutum da magunguna rukunin 𝑨𝒏𝒕𝒊-𝒊𝒏𝒇𝒍𝒂𝒎𝒎𝒂𝒕𝒐𝒓𝒚, da 𝑨𝒏𝒕𝒊 𝒉𝒊𝒔𝒕𝒂𝒎𝒊𝒏𝒆 da kuma 𝒎𝒖𝒍𝒕𝒊𝒗𝒊𝒕𝒂𝒎𝒊𝒏𝒔 in likita yaga bukatar hakan.

Saide kamar yadda kuka sani bana rubuta sunan magunguna a post sai wanda yake 𝘖𝘷𝘦𝘳 𝘛𝘩𝘦 𝘊𝘰𝘶𝘯𝘵𝘦𝘳 (𝘖𝘛𝘊) wato wanda hukumar lafiya ta yadda a iya sayensa koda batare da shaidar takardar likita ba irinsu: paracetamol ko Vitamin c da sauransu.

To amma tunda man da ake shafawa kurajen wanda shike kashe kwarkwatar da kwayayen ba shansa ake ba shafawa ana iya sayensa a chemist da ake kira 𝙿𝙴𝚁𝙼𝙴𝚃𝙷𝚁𝙸𝙽 𝙻𝙾𝚃𝙸𝙾𝙽/𝙲𝚁𝙴𝙰𝙼 5%.

Magani ne na shafawa mai kamar gidan makilin yadda kuke ganin hotonsa akasa... da ake amfani dashi bayan anyi wanka, an kuma tsane laimar jiki da towel. Sai amatso dan kadan ashafe jiki tun daga kasa har zuwa sama agame jiki duk baki daya.

Inkuma jikin yara ne za'a shafa musu ana iya yin amfani da burushi ko tsinken audugar goge kunne domin samun saukin shafa maganin. Hakama idan kurajen sun bayyana har agadon baya ana iyasa wani ya shafawa mutum wannan zaisa kowanne bangare na jiki ya samu.

Sannan bayan shafawar shima me shafawar inya wanke hannu toh ya dangwali maganin yaqara mutsuke hannunsa dashi musamman inda hannu ya shashshafa.

𝐈𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐚𝐛𝐮 𝐈𝐯𝐞𝐫𝐦𝐞𝐜𝐭𝐢𝐧: ana iya amfani da Benzyl Benzoate 25% shima na shafawar ne.

𝐊𝐚𝐫𝐢𝐧 𝐚𝐛𝐮𝐧 𝐥𝐮𝐫𝐚; 

Ayi hankali da lotions din saboda kar maganin ya kasance ya shiga cikin hanci, idanu da kuma baki, a kuma bada muhimmanci wajen ahafawar awasu wurare tsakanin ‘yan yatsu, da kuma kasan kafa, wajen tsakanin ‘yan yatsu na kafa da kuma karkashin farce, haka ma tsakanin duwawu. 

Kuma kada a wanke hannu nan da nan bayan an kammala shafa shi maganin a barshi maganin ya jima.

𝐒𝐚𝐮 𝐧𝐚𝐰𝐚 𝐚𝐤𝐞 𝐬𝐡𝐚𝐟𝐚 𝐦𝐚𝐠𝐚𝐧𝐢𝐧 𝐚𝐲𝐢𝐧𝐢?

Galibi sau biyu ake sawa ayini, saide in likita yaga bukatar ko a iya shafawa sau 3 ayini. Amma de galibi sau biyu ne wato bayan shafa maganin kar akara wani sai bayan kamar awanni goma 12, koma sau 1 ayini wato duk bayan awa ashirin da hudu kwana guda, likitane kadai zai tantance.

Yawancin kan shafa sa safe da yamma. Wato bayan wankan safe dana yamma.

Haka ana iya fara ganin sauki cikin awoyi 48 wato kwana biyu da fara amfani da maganin to amma koda anga sauki to koda ba kullum ba ake shafa maganin, ko kuwa shafasa wani makon mai zuwa..... dalilin hakan shine koda ace da wasu sababbin kwarkwatar hakan zaisa su mutu, ko kuma su samu wata nakasa su gaza tasiri.

Akwai kuma wani maganin anti-parasitic din nasha da akan bayar hatta agangamin lafiya wato "health camp" me suna IVERMECTIN yana zuwa a 200 Microgram. Kwaya tak akeba mutum ya isa bawai za aita sha kullum bane. Na shafawar ne kurum za'a ake sawa sau biyu akalla kwana 3 ko sati guda ko abunda ya sauwaka.

Ana saida su adukkan manya da kananun chemist ana iya samunsa.

Amma de basu kadai bane, kamar yadda nace fashewar kurajen dama wasu cuttukan ka iya haddasa wasu illolin dadai anqara da wasu magungunan rukunin su antibiotics saboda infection da kuma magungunan rage zogi da kaikayi.

Z~~~~~~~~▪︎●●•◇•●●▪︎~~~~~~~~

𝐌𝐀𝐓𝐀𝐊𝐀𝐍 𝐊𝐀𝐑𝐈𝐘𝐀 𝐃𝐀𝐆𝐀 𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑

Cutar na iya bayyana aga tamkar annobarta ake musamman a lokutan zafi. Don haka babbar hanyar da za'a dakile yaduwar da cutar shine gujewa yin gogayya ko kuma hada jiki da wanda ya kamu da cutar, tare da lura da tsafta.

★- Gujewa sanya tufafin dame ciwon yasa, ko kuma kwanciya kan gado ko katifar da masu cuttukan ke kwanciya akai, ko tawul din da wanda ya kamu da cutar yayi amfani dashi.

★- A irin wadannan lokuta idan za'a wanke tufafi to asa ruwan zafi da gishiri aciki awanke. Inkuma ba ruwan zafin to asawa ruwan sanyin gishiri... 

Domin Ita kwarkwatar tana iya kasancewa kwana biyu zuwa uku bayan ta fado kota makale daga jiki, saboda haka akwai matukar bukata kula da yadda za'a kare lafiyar jiki shyasa za'asa ruwan zafi don kar cutar ta sake maimaita kanta.

★- A tabbatar da wanke hatta kayan amfani na shimfidar gado, tawul da kuma filoli, a cikin ruwa mai zafi, akai-akai. kuma ana iya zuba sinadarin bleach ko Omo wajen wankin duk.

★- Bugu da kari kayan sawa ma ya kamata arika goge su, sosai da sosai da dutsen guga na zamani ko na gawayi.  

★- A ma'aurata bai dace ba ace suna saduwa har sai ansamu nasara gamawa da cutar wato bayan gama shan magani... musamman duba da yadda zarar akaji cutar wani gida kan afarga tazo wani gidan.

Allah ya karamana lafiya amin.

Post a Comment

Previous Post Next Post