Iyayen ki suna kokarin ganin sun rufa miki asiri,amma ke ba wannan bane a zuciyar ki damuwar kina kallon rayuwar wasu,wanda sun fi ki sai ki raina abinda iyayen naki suke miki,to ki sani duk wanda zai raina abinda iyayen sa suke masa shike fama da nasani kuma a rayuwar sa.
Dukkan abinda iyayen ki suka miki ki hakura dashi, dukkan abinda iyayen ki suka nuna miki basa bukatar abin nan to don Allah ki hakura dashi Kawai.
Idan har bazaki hakura da abinda iyayen ki suke miki ba,irin hakan ke sakawa fadawa wani hali kuma.
Indai iyayen ki sun baki tarbiyya mai kyau don Allah kiyi kokarin ganin kin tayasu rike wannan tarbiyyar da suka baki
Karkayi kokarin zubar masu da ita, domin ke ma uwa ce watarana,ke ma zaki so ganin yarinyar ki ta miki biyayya ta kula da tarbiyyan da kike bata,to kiyi kokarin fara rabuwa da iyayen ki lafiya.
Duk wanda ya rabu da iyayen sa lafiya lau shine tushen samun kwanciyar hankali sa.
©️ Nusaiba Tasiu Abdulrahim