#CiwonBaya | Bayanka ne ya amsa bayan ɗaga kayan nauyi? To ga abin da ya faru.
Daga cikin raunukan da kan faru ga gadon baya musamman yayin ɗauka ko ɗaga kayan nauyi akwai cirar nama ko tsinkewar naman gadon baya. Cirar nama ko tsinkewar naman na faruwa ne yayin da danƙon naman ya ƙure - ma'ana talewa ko ɗamewar naman to wuce ƙa'idar ɗamewarsa, ko kuma ƙarfin nauyin kayan ya rinjayi ƙarfin da tsokar za ta iya bayarwa bayan ta yunƙura.
A yayin da aka samu wannan haɗari, gadon baya kan amsa, sannan matsanancin ciwo ya biyo baya nan take, saboda cirar nama ko tsinkewar nama a wani sashi na tsokokin gadon baya.
Alamun cirar nama tsinkewar naman gadon baya sun haɗa da:
1. Wasu lokutan a kan ji sautin "ɗas" a daidai lokacin, biyo bayan tsinkewa ko yagewar sashin tsokar gadon baya.
2. Matsanancin ciwo nan take, musamman idan aka sake yunƙurin motsa wurin.
3. Kumburi a wurin raunin.
4. Borin tsoka(muscle spasm) - tsokar wurin kan yi damƙa ko ta riƙa mommotsawa da kanta akai-akai, wanda hakan ke haifar da ciwo ko rashin jin daɗi a wurin raunin.
5. Raguwar aikin gaɓɓan da raunin ya shafa, misali, a kan ji ciwo yayin sunkuyawa, sunkuyawar gefe ko gantsarewa wanda hakan zai sa a riƙa kauce wa irin wannan motsi saboda ciwon.
Da zarar ka samu irin wannan matsala a gadon baya ko sauran gaɓɓai, tuntuɓi likitan fisiyo domin jinyar raunin, har da ma ba ka shawarwari kan matakan kariya don kauce wa faruwar hakan nan gaba.
#BackStrain
#Ergonomics