saboda haka ne ma dukkan bangarorin da ke da hannu wajen ganin an samu lafiyayyiyar dangantakar zaman aure mai gamsarwa ke kokari iya kokari wajen ganin daga

A saboda haka ne ma dukkan bangarorin da ke da hannu wajen ganin an samu lafiyayyiyar dangantakar zaman aure mai gamsarwa ke kokari iya kokari wajen ganin daga bangarensu ba a samu matsala ba

 

         Mijin zai yi kokarinsa wajen ganin ya tsira da mutunci, girma da darajarsa wajen ganin bai tauye matarsa ba a wannan bangare, haka ita ma matar za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin cewa ta gamsar da mai gida a duk lokacin da aka zo tarawa

 

         Wannan kokari da musamman maza ke yi shi ke sanya su a lokuta da dama shaye-shaye abinda suke kira da maganin karfin maza. Wannan kuwa na iya zama na turanci (Viagra) ko na Hausa, irin wadanda za ka ji masu tallan magani a kan tituna da kasuwanni na kwarmata tasiri da ingancinsu

        Sai dai kuma, wadannan magunguna na karfin maza na da matukar illa na kai tsaye ko dai a nan gaba ko kuma a nan take. Misali maganin karfin maza na turanci na bayar da kuzari da karfi ga namiji a lokacin da ya sha, amma illarsa shi ne: Zai kasance idan har mutum ya saba da shansa, in har bai sha ba, ba zai iya tsinana komai ba. Na biyu kuma shi ne, zai takaita rayuwar jima’in mutum

       Shi kuwa maganin Hausa dama dai babu wani bincike mai zurfi da aka yi a kai bare a gane adadin da za sha da zai zama bai yi wa jiki yawa ba. Kuma za ta iya yiwuwa akwai wani adadi na guba a jikin ganye, saiwa ko sassaken maganin da ya kamata a ce an yi waje da shi kafin a sha mai amfanin, amma sai mu dirkawa cikinmu daga bisani wancan guba ya taru ya haifar da wata lalurar ta daban

 

AJIYE BATUN MAGANIN KARFIN MAZA, GYARA CIMARKA

Sau tari abinda ke sanyawa namiji ya gaza wani katabus na a zo a gani a yayin kwanciyar aure na da nasaba da irin abin da ya ke ci. Maza ya kamata ku fahimci cewa wadanan nau’ika na abinci na da tasiri wajen dakile mazantakarku kuma da zarar kun ciresu daga jerin cimarku na yau da kullum, to fa ba sai kun sha wani maganin karfin maza ba, kuma matayenku za su yi murna da ku, kuma har lau babu wata fargaba ta samun matsalar lafiya sakamakon kokarin mutunta gida

Ga nau’ikan abinci da za ka cire daga jerin abincinka ko kuma ka rage su matukar ragewa

 

1-Kayan Toye-Toye

Image result for fry foods

Nau’ikan abincin da aka toya, kamarsu dankali na Hausa da turawa, kayan fulawa da dai sauran abubuwan da ake toyasu da mai na rage karfin sha’awar namiji kai har ma da mace kamar yadda wani bincike na lafiyar jima’i ya tabbatar

A cewar binciken, kayan toye-toyen na nakasta maniyyin namiji ta yadda hakan zai tasirantu wajen hana samun mikewar mazakutarsa yadda ya kamata ko da kuwa an yi masa shafa na sha’awa

 

2. Nau’ikan abincin da ke dauke da sinidarin Carbohydrate .

Image result for CARBOHYDRATE FOODS

Wadannan nau’ika na abinci sun hada da gyararren shinkafa da muke kira da shinkafar gwamnati (shinkafa zazzabar gida ta fi amfani ga lafiyar jiki da na jima’i). Sauran abincin da ke dakushe kaifin mazakuta sun hada da ababaden da ake sarrafa su daga fulawa kamarsu burodi, cin-cin, fanke da dai sauransu. Taliyar indomie da sauran taliyoyi da makaroni duk na iya dakushe kaifin mazakuta musamman idan aka juri cinsu kullum da kullum

 

3. Nau’ikan Lemukan Gwangwani da na kwalba da na jarka

Lemukan na dauke da wani adadi na sikari sama da yadda jiki ke bukata, shi kuma illar sukari na da matukar yawa a jikin dan adam. Da farko dai sikari na karawa mutum kiba, ita kuma kiba na hana namiji kaiwa da komowa a yayin jima’i. Abu na biyu game da sikari dangane da lafiyar al’aurar namiji shi ne, sikari na hana jijiyoyin da ke harba jini zuwa mazakutar namiji a lokacin da ya bukatar haka su yi sanyi

Sikari shi ke jawo matsalar nan da ake kira da illar sikari wato Sugar Crash a turance. Idan wannan matsala ta faru, duk tabawar da mace za ta yi wa namiji ba zai mike ba ko da kuwa yana so a ransa ya yi jima’i

 

To, mazaje, sai a kula wajen tantance mai za ci don a tsira da lafiyar jiki da lafiyar aure. Mun gode

Post a Comment

Previous Post Next Post