sallah kasru

 *SALLAR KASRU.*
(SALLAR MATAFIYA).

a. Ma’anan sallar Kasru.

 Sallar kasru a halin tafiya: Ita ce rage sallah mai raka’a hudu zuwa biyu. Kuma wannan akwai ma’ana mai girma wacce Shari’ar Musulunci ta kunsa na daga abin da zai kiyaye rayuwar musulmi, da kuma tabbatar da sauki a gareshi. Kasru ya tabbata ne ta Akur’ani da Hadisi, kuma ya halasta akan ittifaki na malamai.
: b. Kasaru ana yin shi ga duk tafiya ta aminci ko wani ta.

Ana kasaru ne a halin tafiya cikin aminci ko tsoro, tsoro wanda ya tabbata a ayar da ta gabata, ya zo ne a galibin lokaci, domin hakika abin da yake shi ne mafi rinjaye a tafiyetafiyan Annabi ﷺ‬ ba’a rasa tsoro a ciki, domin ganin sallar bata kubucewa akan tsoro Sayyidina Aliyu ya ce wa Sayyidina Umar (Allah ya kara musu yarda) : za mu yi kasaru alhali mun aminta, sai Sayyidina Umar ya ce masa: “Na yi mamakin abin ka yi mamakin sa, sai na tambayi Manzon Allah tsira da aminci Allah su tabbata a gareshi ya ce: “Sadaka ce da Allah ya yi muku ita, saboda haka ku karbi sadakarsa”. (Muslim ya ruwaito shi).
[ Nisan dake sawa a yi sallar kasaru.

 Amma nisan dake sa wa a yi sallar kasaru to shi ne duk abunda aka ambace shi a matsayin tafiya wacce aka sani, kuma ana daukar masa guzuri da abin gusuri.

d. Inda ake fara sallar kasaru.

 Matafiyi yana fara yin kasru ne idan ya bar gidajan garin sa, na abunda za’a kira shi da sunan mararraba a al’adance, domin Allah madaukakin sarki ya sanya sallar kasaru idan ana tafiya a bayan kasa, tafiya kuma bata kasancewa har sai matafiyi ya rabu da gidajan garinsa.
[ *HADA SALLOLI BIYU.*

 Hada sallaoli biyu sauki ne da yake bijirowa a lokacin bukata shi, hakika mafi yawan malamai sun so barin hada salloli biyu sai dai a lokacin bukatawa wacce take bayyananna, domin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai hada tsakanin sallah da sallah ba sai lokuta kadan. Kuma duk wanda ya halasta ya yi kasaru to ya halasta a gareshi ya hada salloli biyu, amma kuma ba duk wanda ya halasta ya hada salloli ba yake halasta a gareshi ya yi kasaruba Hada a farkon lokaci da kuma karshen lokaci.

 Abin da yafi falala shi ne mutum ya aikata abin da ya fi sauki a gareshi na hada sallolin kodai a farkon lokaci (Jam’u Taqdee) ko kuma a karshen lokaci (Jam’u Ta’akheer), domin abun nufi anan shi ne sauki da saukakawa. Amma idan jam’in suka yi daidai (wato kowanne aka yi babu takura) to abunda ya fi shi ne a jinkirta zuwa lokacin sallah ta biyu(wato: Jam’u Ta’akheer), idan kuwa ya kasance ya isa to abunda ya ke shi ne Sunnah ya yi kowacce sallah a lokacinta.

Post a Comment

Previous Post Next Post