fried rice

*PROWN FRIED RICE BY Gloden KITCHENπŸ‘¨πŸΎ‍πŸ³πŸ‘©πŸΎ‍πŸ³πŸ²πŸœπŸπŸ›πŸ₯£*

Abubuwan hadawaπŸ‘‡πŸΎ
Man gyada
Thyme
Bay leaves
Shinkafa
Chicken seasonings
Gishiri
Naman kaza (optional)
Shrink🦐(optional)
Citta
Tafarnuwa
Albasa
Green beans
Attarugu 
Tattasai
Karas
Masara(yar shago)

Zaki wanke Naman kazar,ki tafasa da gishiri da kayan kamshi ki soya sama-sama ki ajiye,sai ki Yi marinating shrink naki,shi ma ki soya sama-sama ki ajiye gefe daya. ki zuba mai a tukunya ki saka thyme,gishiri,bay leaves 2, ki zuba danyar shinkafar ki ki soya su ta hanyar juya su for like 5mins Sai ki zuba ruwa akai tare da gishiri da sinadarin dandano,ruwan daidai Wanda zai dafa maki ita,ki rife domin ta dahu... Ki wanke tare da yanka wadancan kayan lambun gutsi-gutsi ki ajiye. 
Bayan ta tsane ruwan tas,zaki zuba mai a wani pan/pot ki zuba yankakkiyar albasar ki,jajajgen citta da tafarnuwa,ki soya na 2mins Sai ki zuba wancan kayan lambun da aka yanka akai,ki juya su, ki saka chicken seasonings (maggi amma na kaza/yellow Maggi's) ,Curry, Sai ki zuba shinkafar akai,a saka masarar tare da Naman kazar ki juya su komai ya hade jikinsa Sai ki rage wutan ki rife tukunyar domin su karasa dahuwa. Shikenan an kammala 


Post a Comment

Previous Post Next Post