Matakai Bakwai Domin Rage Haɗarin Kamuwa Da Kansar Mama — World Health Organization (WHO)
Hukumar Lafiya ta Duniya, wato WHO a taƙaice, ta ce mata miliyan 2.3 ne suka kamu da kansar mama a shekara ta 2020 kawai, inda cutar ta hallaka mata 685,000 a duniya. Kuma zuwa ƙarshen 2020, akwai mata miliyan 7.8 da aka gano suna rayuwa da cutar cikin shekaru biyar da suka gabata, wanda hakan ya sanya kansar mama cutar kansa mafi yawa a duniya.
Kansar mama ba ƙwayoyin cuta ne ke haddasa ta ba kuma ba cuta ce mai yaɗuwa ba. Kansar mama na faruwa ne sakamakon rikiɗewar ƙwayoyin halittar mama.
Duk da cewa kansar mama ba ta yaɗuwa daga wani zuwa wani, amma tana iya bazuwa zuwa sassan jiki. Kuma mata na mutuwa ne daga cutar sakamakon fantsamar ta zuwa sassan jiki.
Kusan rabin kansar mama na faruwa ne ga mata ba tare da wani haɗarin kamuwa ba face kasancewa jinsin mace da kuma shekaru sama da 40.
Sai dai, haɗarin kamuwa da kansar mama na ƙaruwa da abubuwa kamar haka:
1. Shekaru fiye da 40.
2. Ƙiba / teɓa.
4. Gado: matan da iyayensu ke da kansar mama na da ƙarin haɗarin samun cutar.
5. Shan taba sigari ko amfani da taba domin sinadari.
6. Shan hasken radiyeshin, kamar 'x-ray'.
7. Amfani da magunguna domin dawo da sinadaran haihuwa bayan mace ta kai shekarun daina haihuwa.
Matakai da hanyoyin da za su taimaka wajen rage haɗarin kamuwa da kansar mama sun haɗa da:
1. Shayarwa: Haɗarin kamuwa da kansar mama na raguwa da tsawon lokacin da mace ta shayar.
2. Motsa jiki ko atisaye akai-akai.
3. Daƙile ƙiba / teɓa.
4. Ƙaurace wa shan taba, shaƙar hayaƙin taba da dangoginta.
5. Ƙaurace wa barasa / giya da dangoginta.
6. Ƙaurace wa magunguna jinsin 'hormone'. [Ana amfani da magunguna jinsin 'hormone' domin ɗaƙile ko yi wa sinadarai masu sarrafa jiki ƙaimi kamar sinadaran haihuwa, sinadaran ginin ƙashi da sauransu]
7. Ƙaurace wa radiyeshin kamar hasken 'x-ray' da sauran jinsinsa.
Sai dai, ko da za a iya kiyaye waɗannan hanyoyi duk