- Beef
- Albasa
- Tarugu
- Maggi
- Veg. Oil
- Kayan kamshi
- Step 1
Ki wanke nama sosai ki dora a wuta. Ki zuba kayan kamshi da albasa ki rufe ki barshi ya dahu sosai. Ki zuba maggi da salt.
- Step 2
Idan ya fara narkewa da kanshi sai ki sauke.
- Step 3
Ki nemi turmi ki jajjaga tarugu da albasa. Ki zuba maggi sannan ki saka naman ki hau daka.
- Step 4
Sai ya daku sosai sannan ki dora mai a wuta mawadaci.
- Step 5
Idan ya yi zafi sai ki juye naman ki rage wutar.
- Step 6
A hankali kina juyawa yana soyuwa har sai ya yi golden brown sannan ki kwashe.
- Step 7
Ki nemi mataci ki zuba a ciki, sannan ki dora abu mai nauyi ki barshi ya kwana a haka duk man jiki ya fice.
- Step 8
Serve.