Illolin Yawan Shan Sukari (Sugar)
Mene ne Sukari?
Sukari dai wani sinadari ne da ake amfani dashi wajen sa ma abubuwan sha ko ci zaƙi domin inganta daɗin su a baki.
Sukari na iya kasancewa suga da ake samar da shi daga rake irin wanda muke amfani da shi kullum ko kuma wanda ake haɗa shi a dakin bincike (Laboratory), watau "chemical sugar", irin wanda ake sawa a Lemun Kwalba/Roba (Soft/Soda Drinks, Cakulet (Chocolate) da sauransu.
Manyan Illolin Yawan Shan Sukari (Sugar)
1. Yiwuwar Kamuwa Da Ciwon Sukari (Type 2 Diabetes)
Shan sukari da yawa na haifar da turjiyar sinadarin sarrafa sukari a jiki, INSULIN, watau "Insulin Resistance", hakan na iya haifar da ciwon sukari.
2. Ciwon Hakora
Kwayoyin cutar dake cikin baki masu haifar da ruɓewa, rami/kogo da ciwon hakora na rayuwa ne da sukari, shi ne abincin su.
3. Matsala Ga Lafiyar Zuciya
Binciken Masana ya tabbatar da alaƙa tsakanin samun matsalar ciwon zuciya/Hawan Jini, kumburin zuciya da yawan shan sukari.
4. Matsalar Sarrafa Sinadarai A Jiki (Metabolic Syndrome)
Yawan shan sukari na taimakawa wajen haifar da matsalar sarrafa sinadarai na abinci, wanda hakan na bayyana ta samun TUMBI, KITSE MAI YAWA A JIKI da HAWAN JINI.
5. Hanzarta Yiwuwar Samun Ciwon Daji (Cancer)
Akwai nau'in ciwon daji (Cancer) da aka tabbatar da yawan shan sukari na taimakawa wajen gaggauta kamuwa da su. Wannan ya biyo binciken da masana sukayi akan wasu mutane dake ɗauke da irin ciwon.
6. Matsalar Cutar Ƙiba (Obesity)
Shan sukari da yawa na cikin abubuwan dake iya haifar da haɓaka na jiki ta yanda bai dace ba, wanda hakan na iya haifar da cutar ƙiba.
7. Ciwon Sabo (Addiction)
Yawan Shan Sukari ba bisa ka'ida ba na saba ma da jiki bukatar sukari ɗin, wanda hakan na iya sa mutum zai ji shi sai a hankali in bai sha abu mai sukari ɗin ba, ko da lemun kwalba ne.
Shan sukari daidai gwargwado baya haifar da waɗan nan matsalolin, amma yawan shan shi ko da a lemun kwalba ne da sauran kayan kwalba/gwangwani, na iya haifar da ɗaya ko duka matsalolin.
Wannan yanayin baya faruwa FARAT ƊAYA, a hankali a hankali yake ginuwa har matsalolin su sauka.
Sunana Pharm. Musa A Bello ɗan Zaria, Baban Fatima da Abdulwahab, Mijin Hafizatul Qur'an Na'imatu.