Abubuwan da ke jawo warin baki da hanyoyin magance shi:
Warin baki, matsala ce da masana suka yi imanin tana damun kusan kashi 25 cikin 100 na al'ummar duniya. Akwai abubuwa da dama da ke haifar da matsalar, sai dai yawancin suna da alaka da tsaftar baki.
Warin baki na sanya damuwa da yarfa mutum a cikin jama'a, baya ga tsarguwa da damuwa da masu shi ke tsintar kansu a ciki, sai dai abu ne mai sauki shawo kan wannan matsala.
Mujallar cibiyar lafiya ta MNT ta fitar da wani tsokaci, wanda zai taimaka wa masu warin baki, wajen shawo kan wannan matsala da suke fama da ita.
Mujallar Medical News Today ta shafin intanet ta yi kiyasin cewa mutum daya cikin hudu na fama da warin baki a-kai-a-kai.
Warin baki shi ne na uku cikin jerin dalilan da kan sa mutane su je neman kulawa wajen likitan hakori, wato bayan ciwon hakori da ciwon dasashi kenan.
Warin baki gama garin matsala ce da kan jawo wa wasu damuwa sosai da rashin sakewa. Sai dai a lokuta da dama wasu ba ma sa sanin cewa bakinsu na wari, sai dai na kusa da su ya ji.
Yana sanya mutum ya ji kunya musamman idan ya san an gane bakinsa na yawan wari.
Akan ji warin bakin mutu tun daga nisa mita hudu a lokuta da dama.
Nau’ukan abincin da ke gusar da warin tafarnuwa
'Mayukan goge baki na gawayi ba su sa hasken hakora':
'Da kasa nake wanke baki na'
Me ke janyo warin baki?
Ana iya samun warin baki idan ba a wanke baki da kyau, wani lokaci kuma ya na iya zama dalilin rashin lafiya.
Haka kuma, akwai wasu nau'uka na abinci da ka iya sa warin baki. Sannan wasu dabi'u na yau da kullum ka iya janyo wa mutum warin baki.
Matsala ce da ke damun mutum 1 cikin mutane 4
Baban abun da ke kawo shi shi ne rashin tsaftar baki
Barin ragowar abinci, ko makalewar wani a ciki na haifar da matsalar
Rubewar haƙori musamman daga can cikin baki
Barin baki a bushe ƙarƙaf saboda yawu kan taimaka wajen sa baki ya dan yi wasai
Shan taba da su wiwi na jawo warin baki sosai
Akwai kuma yanayin da magungunan da ake sha na asibiti kan sa baki wari amma na dan lokaci ne zuwa sanda za a daina shan maganin.
Akwai kuma ciwon da ke shafar maƙogoro da hanci da baki inda ƙwayoyin cutar ke ruɓewa su janyo warin baki
Abinci dangin su tafarnuwa da albasa da kayan zaƙi kan taimaka wajen sa baki wari.
Warin baki
Ta yaya za ku magance matsalar?
Hanya ta farko ta magance warin baki ita ce kula da tsaftar bakin ta hanyar yin buroshi a kai-a kai bayan cin abinci da lokacin kwanciya. In ba halin buroshi a daure a dinga yin asuwaki ko kuma kuskure bakin duk lokacin da aka ci wani abu, kamar yadda likitoci suka fada.
A dinga zuwa ganin likitan haƙori a kai-a kai musamman don su za su fi gano ko akwai haƙorin da ya ruɓe wanda ka iya jawo warin bakin. Ganin likitan haƙori sau biyu a shekara ya wadatar.
Yana da kyau a dinga kurkure bakin da ruwan ɗumi da gishiri don yana kashe ƙwayoyin cutar da ke bakin waɗanda ka iya jawo wari.
A dinga yawan sakace don cire ragowar abincin da ke maƙalewa a bakin.
Idan aka zo buroshi a dinga wanke kan harshe da kyau
A guji barin baki ya bushe. Yawaita shan ruwa na rage hamamin baki ko da kuwa an yini ba a ci komai ba.
A guji shan taba ko sauran kayan hayaƙi da na maye
Tauna cingam ko alawa musamman marasa zaƙi na taimaka wa wajen sa baki ya yi wasai ba za a ji warinsa ba
Idan mutum duk ya gwada waɗannan matakan a gida kuma baki bai daina wari ba to akwai buƙatar ya ga likita, ba mamaki wani haƙori ne ya ruɓe a can ciki da yake buƙatar a cire shi.