YADDA AKE HADA SABULU NA MUSAMMAN DOMIN GYARAN FATA DA GYARAN FUSKA DA KUMA HADIN DILKA.

YADDA AKE HADA SABULU NA MUSAMMAN DOMIN GYARAN FATA DA GYARAN FUSKA DA KUMA HADIN DILKA. 

1) DOMIN KYAWUN FUSKA

     A samu:-
1 . Garin zogale
2 . Farar albasa
3 .Sabulun ghana 
4 . Sabulun Dettol
5 . Sabulun salo
Yadda za a hada. 

Ki samu sabulun ghana dana   salo dai dai kai daya sai ki samu dettol shima kamar guda 2 sannan sai ki sami garin zogale cokali 2 sai albasa manya guda 2 duk sai ki hada su a turmi ki kirbe su sannan sai ki juye a roba mai murfi zaki dunga wanke fuskarki da shi yanada kyau sosai  yana magance kurajen fuska. 

2) HADIN DILKA

1 . Dilka da sukari
2 . Lemon tsami
3 . Man zogale
4 . Turaren Du'aul jannah 

   Yadda za a hada:-

Zaki zuba duk kayan a cikin ruwa sai ki sa wuta amma kadan  har sai  ya tafasa yayi kumfa sai ki sauke idan ya huce kirinka dangwala  kina shafawa a ko ina a jikinki, ki bari ya bushe, zai fara murmushewa da kansa sai ki karasa murje shi sai kiyi wanka da ruwan dumi, fatarki zatayi kyau

3) SABULU NA MUSAMMAN
  A samu:-
1 . Madarar turari
2 . Lalle da dilka

Post a Comment

Previous Post Next Post