YAN UWA MAZA KAR KUYI WASA DA WANNAN HADIN

'YAN UWA MAZA KAR KUYI WASA DA WANNAN HADIN

Indai kai na miji ne, ko waye kai, ko kafi kowa kwarewa a aikin Likita, kar ka yadda ka zauna baka yin wannan hadin da kuke gani a hoto

Kullun kai ne cin maggi da kayan dandano a girki, kai ne shan kayan zaki da lemon kwalba mai gas, kasha wannan kasha wancan, zaki ya taru maka a mara, baka motsa jiki, kullun kana cikin shan ruwan sanyi, tafiya nan da can akan abin hawa, a gida sanyin AC, a mota sanyin AC, haka a office sanyin AC ke bugaka, sanyi ya mayar maka da gaba kamar lagwanin fitila, tabbas kana cutar da kanka ne dan uwa, Malam ba zaka taba yin lafiya da kwazo ba
A gurin raya Sunnah ta Ma'aiki (SAW) minti biyu kacal ka fado kasa kamar Zakara, Dole matarka ta rena maka, idan bata da karfin imani dole ta fara bin mazan banza, wannan hadin da kuke gani shine maganin matsalarka dan uwa

Tuzurai bana goyon bayan kuyi wannan hadin, amma ga duk wani tuzuru da aka saka ranar aurensa ya tabbata yayi wannan hadin, yafi duk wasu magunguna da zakayi amfani dasu tasiri, zai wanke maka mara tas, zakayi karfi garau

Tafarnuwa ne, da Kajiji, da kanumfari, da citta danye mai yatsu, za'a bare tafarnuwan, cittar za'a tsagata gida biyu, sai a wanke kajijin da kanumfari a cire kasan dake jikinsu, sai a hadasu gaba daya a zuba a cikin bokiti ko wani roba mai murfi da aka cikashi da ruwa mai tsafta, a barshi sai yayi kwana daya kafin a fara sha

Duk lokacin da kasha kofi daya sai ka sake mayar ruwa cikin kofi daya a kai, haka za'a dinga sha kowani lokaci har sai dandanonsa ya  kare, a kalla duk bayan wata biyu kayi wannan hadin, kudinsa bai wuce 2K ba

Don Allah dan uwa Magidanci ka kasance mai yawan yin wannan hadin, Wallahi zaka tuna da Datti Assalafiy, kuma zaka sanya wa Datti albarka a matsayin tukwicin godiya

Idan da matarka tana maka raini zata dawo yi maka ladabi da biyayya, idan ka fita daga gida duk bayan awa daya zata kiraka ta tambayi lafiyarka, Allah-Allah take ka dawo gida, kai karan kanka zaka san cewa kai yanzu na miji

Post a Comment

Previous Post Next Post