KINADA JINNUL ASHIQ?
ME YASA DUK WANDA YAZO NEMAN AURENKI DA MAGANA TAFARA TAFIYA SAI ABUN YA RUSHE KODA KUWA ANSAKA RANA?
KINA DA MATSALAR RASHIN HAIHUWA?
KO MATSALAR NA NAMIJIN DARE
NEMAN TAIMAKO
A Wannan lokacin kashi 70% a cikin 100% na mata suna dauke da matsalar jinnul Ashiq wato aljannun soyayyah batareda sunsani ba dukda cewa akwai alamomin da mace zata gane tana dauke da matsalar
Da yawa sukanyi takaici tareda kuka akan damuwar batare da sanin menene abinda yasa hakan ba
Akwai wasu nauikan jinnu da ake kira jinnul Ashiq wato Aljannun soyayyah wadanda sau da yawa basu nunama mace suna jikinta shisa wasuma ko anfadamasu matsalan jinnuh ce.zasu karyata
Su wannan aljannu basu taba tashi ga mace ko su nuna kansu saidai alamomi ke.nuna mace na dauke da wannan aljannuh kuma matukar mace bata rabu dasu ba bazasu taba barin tayi aure ba koda kuwa ta tara samari sunkai 1000
Babban matsalan shine da dama Wannan aljannun sun auresu ta hanyoyi daban daban ammah basu sani ba balle su magance
Wasu kuma sai bayan sunyi aure aljannun ke shigarsi ta hanyar kawo Fada a tsakaninsu zaki samu kullim cikin fada,Rigima da rashin kwanciyar hankali babu dalili duk alamomine na jinnul ashiq sukan juyama mace Mahaifa ta yanda zata dena haihuwa ko bazata haihu ba wasu kuma kamar yan mata sukan haiparmasu da
Rashin Masoya
Rashin Aure
Lalacewar Maganar aure
Fandarewar 'ya'ya
Infection mai yawa
Rikicewar Al-ada da sauransu
Wannam aljannu mace zata iya gane tana tare dasu ne kkawai ta hanyar alamominsu gasu zan fada
**Yawan Ciwon Kai
**Yawan Ciwon Mara
**Yawan Ciwon Ciki
**Yawan Ciwon Kafafu
**Yawan Faduwar Gaba
**Yawan Fushi babu dalili
**Wani lokacin baayima mace komaiba sai bacin rai
Akwai alamomi sosai ammah shawara matuqar kinada wannan matsala zaki iya neman taimakonmu ko karin bayani a
NAMIJIN DARE A RAYUWA MU
Abin da ake nufi da namijin dare shi ne wani aljani da ake kira Jinnul Ashik wanda ke sa mace ta wayi gari tana yawan yin mafarki wani na saduwa da ita cikin barci, wannan al’amarin ya kasance ya yi yawa a tsakanin mata kuma har ya kai ga wasu cututtuka suna faruwa ga mace ko namiji ko kuma cututtukan da ba sa jin magani a yi ta wahala har a gaji.
Wadanne Abubuwa Ke Kawo Samuwar Jinnul Ashik
Malaman duniya sun bayar da fatawowi cikin Alkur’ani da hadisan Annabi(SAW), kamar cikin Majmu’ul fatawa na Shaikul Islam ibnu Taimiyyah da littafin Ash-shifa’u bil kur’an minal jinnu wash shayadini na Ridha Ash-sharkawi da littafin Minhajul kur’an li’ilaj as-hir wal massi as-shaidani suka ce:
Wannan Aljani da ake kira jinnul Ashik yakan samu mace ta hanyoyi hudu kamar haka:-
1: Wata shi yake kawo kansa saboda rashin kyautata sutura da shigar banza na kayan zamani, wanda musulunci ya hana.
2: Wata kuma ita take kai kanta inda aljanun suke, kamar zuwa wajen bokaye.
3: Wata kuma sihiri aka yi mata saboda ta hada nema da wani maras tsoron Allah.
4: Wata kuma tana kyautata sutura, tana bin Allah, amma Allah zai jarrabe ta da wannan shaidani.
A takaice dai wadannan hanyoyin da shi wannan shaidani zai zo wajen ta sai ya mayar da abin ya koma zuwa soyayya ya raba ta da kowa ya hanata yin aure ko ya rabata da mijinta ko ya hanata zaman lafiya da shi, shi kuma Aljanin ya ci gaba da zama da ita yana saduwa da ita ya dauke ta kamar matarsa kuma ya hana mijinta komai da ita, ya sa gaba da kiyayya a tsakani. Allah ya kiyaye.
Hanyoyin Da Yake Bi Ya Zo Wa Mata A Matsayin Mijin Dare Su Ne kamar Haka:-
1: Yakan zo wa mace cikin barci ya dinga saduwa da ita cikin mafarki, ta fuskar mijinta ko wani wadda take jin kunya ko wadda bata sani ba ko dan uwanta ko ta siffar mace ‘yar uwarta.
2: Yakan zo mata a siffar mijinta yana saduwa da ita a zahiri ba a mafarki ba, amma kuma shaidani ne ba mijinta ba ne.
3: Yakan zo wa mace tana kwance ta ji kamar ana saduwa da ita, ita ba mafarki ba, ita kuma ba idon ta biyu ba.
4: Wata macen ta kan kwanta ta yi barci ba wadda ya sadu da ita, amma idan ta farka ta wayi gari sai ta ga kamar wani ya sadu da ita.
Alamomin Da Za A Iya Gane Namijin Dare
Daga cikin alamomin da mace zata gane tana da wannan matsalar shi ne:-
Shi wannan shaidanin zai dinga zuwa yana saduwa da ita cikin barci, yawanci mata suna tsintar kansu cikin wannan yanayin, amma sai su dauka shirmen mafarki ne kawai, to a gaskiya ba haka bane.
Duk mata ko budurwar da take irin wannan mafarkin za ka same ta tana fama da wadannan matsalolin, ko da za ka tambaye ta
wadannan matsalolin za tace maka tana fama da su. Daga ciki akwai:-
1: Bacin rai ba a mata komai ba, ta ji tana jin haushin kowa har ma da mijinta ko kuma ta ji kamar mijin ya sake ta, ta gaji da auren, da za ka tambayeta laifin mijin ba zata fadi laifinsa ba, wata rana ma ta ji tana tsanar ‘yan’yanta.
2: Yawan ciwon kai daga lokaci zuwa lokaci kuma baya jin magani.
3: Tsananin ciwon kirji da ciwon baya.
4: Tsananin ciwon mara lokacin al’ada da kuma zubar wani ruwa daga farjin mace, shi ba al’ada ba ne, kuma ya kasu kashi 2; mai yauki da maras yauki ko mai kauri kamar koko tare da yawan kaikayi ko fitowar kuraje.
5: Ga yawan zubar ciki ko bari, ko kuma rashin samun ciki, amma za ta iya kasancewa ta dauki alamomi na masu ciki har ma ana zaton tana da ciki, amma ana kwana 2 sai ta canza kamar ba ciki ba, ko ta rinka yawan mafarki ta haihu.
6: Idan mijinta yana saduwa da ita tana jin zafi, ko kuma yana saduwa da ita ba zafi, amma bata samun biyan bukata.
7: Daf da magariba ta dinga jin zazzabi ko faduwar gaba ko yawan tsorata, ko kasala da bacin rai.
8: Idan ta dauki Alku’ani za ta karanta sai ta dinga jin kasala da hamma da hawaye da barci da zarar ta ajiye kur’anin sai ta ji wartsake kamar ba ita take jin barci ba.
9: Sannan kuma ko ta kwanta tana son yin barci sai ta kasa, ta yi ta juyi ta kasa barci, mijinta na zuwa kusa da ita sai ta dinga samun firgita da tsoro.
10: Ko ta wayi gari gashin kanta ya dinga kadewa ko ya yi ja, bakinta ya dinga bushewa ko ya yi ja.
11: Yawan kaikayin ido da kaikayin kai na amosani, amma ba amosani ba ne.
12: Yawan kaikayin kunne da yawan kaikayin hanci kamar mura, amma ba mura bane, ko yawan kumburin ciki.
13: Yawan zubar jini da ba na al’ada ba, ko jinni ya rika yi mata wasa. Sannan kuma har ma wacce ba ta da aure.
budurwa ko bazawara za ta iya samun wannan matsalar, amma ita bambancin da ke tsakani da ita wacce take da aure shi ne kamar haka:-
14: Ita marar aure za ta kasance duk lokacin da wani ya zo wajen ta da maganar aure kamar za a yi sai abin ya lalace daga wajen ta ko daga waje