NASIHARMU TA YAU:*______________________



*NASIHARMU TA YAU:*
______________________

Ya ku yan uwana a musulumci ina son tunatar da mu a kan wani gagarumin abu dake cikin rayuwar mu wanda wasu daga cikin mu bamu dauke shi a bakin komai ba. Mu sani cewa duk girma da yawan bautar da zamu yi wa Allah Subhanahu wa ta'ala ba zai yafe mana hakkin wani ba. Har sai dai in shi wanin nan ne ya yafe mana. Wannan babbar magana ce. Masifa ce gagaruma idan aka yi duba da rayuwar da muke yi yanzu. Wani zamu bata mishi rai mu bakanta mishi. Mu bata mishi suna alhalin bamu ma san shi ba. Bamu san komai a kanshi ba. Mu ambace shi da abin da ba halin shi bane wanda kuma tabbas ne Allah sai ya hukunta mu a kan wannan abin. Wannan shi ne abin da wasu basu sani ba. 
Abu mafi muni kuma sai Allah ya jarrabe mu da girman kai. Sai ya kasance koda daga baya mun san mun zalunci mutum ko mun zarge shi da abin da ba halin shi bane sai mu ji nauyin rokon gafarar shi. 

Ya yan uwana a musulumci ina tunatar da mu ne a kan girman masifar dake cikin cin hakkin wani. Dan Allah mu yi kokarin kiyayewa. Mu sani komi girman laifinmu in dai tsakanin mu da Ubangijinmu ne muna sa ran yafiyarsa in mun neme ta. Mu yi kokari mu nemi yafiyar yan uwanmu da muka san akwai hakkokinsu akan mu. 

Garkuwar Mata Nasmat ✍️.

Post a Comment

Previous Post Next Post