Alamu Biyar Na Fara Ruɓewar Hannu Bayan Ɗorin Gida.

Alamu Biyar Na Fara Ruɓewar Hannu Bayan Ɗorin Gida.

Ɗorin gida ko gargajiya na iya janyo mummunan lahani ga tsokoki, jijiyoyi jini, jijiyoyin laka, haɗi da ƙashin kansa. Hakan na faruwa ne sakamakon katsewar gudanawar jini saboda ɗaurin ɗorin.

Lahani na fara faruwa daga awa uku zuwa shida bayan ɗaurin da ya katse gudanawar jini a gaba da ɗaurin.

Idan katsewar jini ta zarce za ta haifar da ruɓewar hannu ko ƙafa wanda daga ƙarshe zai tilasta yanke sashin a asibiti ɗungurugum!

Amma akwai alamomi biyar da za su taimaka wajen gane katsewar gudanawar jini ta faru kuma hannu ko ƙafa ta fara ruɓewa.

Alamomin suna fara bayyana tun daga awa ukun farko kuma sun haɗa da:

1. Matsanancin ciwo a gaba da ɗaurin karayar.

2. Shanyewar hannu/ƙafa: A yayin da jijiyoyin laka suka samu lahani, hannu/ƙafa zai shanye, wato rashin ƙwari zai bayyana sannan mutum ya gaza motsa yatsun hannu/ƙafa.

3. Gushewar ji a fata: Idan aka taɓa hannu/ƙafa mutum ba zai ji ba, ko kuma ya riƙa jin dindiris, sagewa, jin kamar shokin ko kuma kamar ana tsitstsira allura.

4. Koɗewa: Hannu/ƙafa zai koɗe ko kuma ya ɗashe. Hakan na nuni ga ƙamfar jini a sashin.

5. Ɗaukewar bugawar zuciya: Akwai wasu sassa a jiki da ake  iya jin yadda zuciya ke bugo jini zuwa sassan jiki, wato 'pulse'. A hannu, ana iya jin bugawar zuciya a kan gaɓar gwiwar hannu da kuma tsintsiyar hannu daidai ƙasan babban yatsan hannu. Haka nan, ana iya ji ƙafa a kan tafin sawu. Duba "comment section" domin gani wararen da za ka iya jin bugawar zuciya.

Da zarar waɗannan alamomi sun fara bayyana a garzaya asibiti domin ceto hannu/ƙafa daga ruɓewa. Amma idan aka yi buris, daga ƙarshe zai tilasta yanke hannun/ƙafa a asibiti. Yanke wani sashin jiki na nufin nakasa.

#TBS
#Fracture 
#Gangrene

Post a Comment

Previous Post Next Post