Ko Kin San Da Kanki Za Ki Iya Tunzura Mijinki Ya Nemi Mata A Waje?
Wasu mazan suna fadawa neman mata ne, saboda sun auri ballagaza shashashar mace, wacce ba ta iya zaman aure ba, wacce ba ta iya kissa da tarairaya ba. Wacce ba ta san me rayuwar aure ya kunsa ba. Ita dai kawai gatanan ne. Babu kwalliya wa maigida, babu shafa turaruka masu kamshi da gyara fata, ba ta shafa mai wanda zai sa fatarta ta yi laushi, ba ta gyara gashin kanta, ba ta iya kwanciyar aure ba, ba ta iya shagwaba mai fisgar hankali ba, ba ta iya nuna kauna da soyayya ga miji ba. Ba ta iya zama ta yin abubuwan da zai sa ka mijinta nishadantu ba. Ba ta iya magana ba, ba ta iya kallo ba. Ita dai ga ta nan ne kawai.
To kun ga mijinta baya samun abin da ya kamata ya samu a wurinta, mai ya yi saura? Sai ya je ya fara biye-biyen mata idan baya jin tsoron Allah. Kin ga kina daya daga cikin mutanen da suka ba shi gudunmuwa wurin jefa shi cikin wannan musiba ta neman mata.
Wani kuma yana fadawa neman mata ne, saboda mabukaci ne dayawa, ita kuma matar ba ta iya jure masa, har ya kai ga duk lokacin da zai neme ta sai an yi rigima, to a nan idan mijinki ya bukaci karin aure, kada ki hana shi, idan kuma kika yi masifa kika tayar masa da hankali, toh zai kuwa fada neman mata, kina zaune zai kawo miki tsarabar HIB/AIDS har cikin dakinki. Don haka ki kyale shi ya yi aurensa don wani baya iya hakuri da mace daya.
Wata kuma ta iya kwalliya da kissa da tarairaiya da abinci da tsabta, ta iya kwanciya da komai, amma mijinta kuma manemin mata ne, to irin wannan sai a ce jarabawace, domin irin wannan mazan ko mata dari za a tara musu to ba zai hana idan sun ga wata su nema ba. Domin su ba su dauki aure a bakin komai ba. Ki dage sosai da rokon Allah, sannan kada ki fasa abin da kike masa na kyautatawa, ki ci gaba da izinin Allah zai dai na wata rana. Sannan ki rinka kokarin nuna masa illan yin hakan, misali: Ki ce wane idan ni kadai ba na isan ka ne, to ni babu damuwa ka karo wata, saboda ina ji maka tsoron cuta, kuma