HADDAN ALQUR'ANI Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh, Shi haddan Alqur'ani a ko da yaushe, abubuwa hudu (4) yake buƙata. Waɗannan abubuwan ko sune:

.               HADDAN ALQUR'ANI 

Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh, 

 Shi haddan Alqur'ani a ko da yaushe, abubuwa hudu (4) yake buƙata. Waɗannan abubuwan ko sune:
1. NIYYA:
Na farko shi ne ya kasance mutum shi ke da ra'ayin yin haddar. Ko ba komai, sa kai yafi ɗauka. Idan kuma yaro ne Wanda bai san ciwon kansa ba, toh ya kasance yana samun cikakken kulawa, ma'ana, jan ra'ayi da sa ido. 

2. LOKACI:
Dole ne mai kwaɗayin haddar Alqur'ani ya zamo yana da lokaci da zai keɓe na yin karatu a kowace rana ko da sa'a guda ɗaya ne kacal. Kuma ya tabbatu akan hakan. Idan sa'a ɗaya yake da shi, sai ya zamo yana anfani da rabin sa'a domin ƙarin hadda, ɗayan rabin kuma ya yi muraja'ar tsohon hadarsa. Domin sau da yawa, matsalar raunin hadda yana samuwa ne ta hanyar tara hadda har ya yi yawa sannan wai a fara tunanin gyaran hadda. Abin so shi ne idan mutum ya ce yau ya haddace izu daya, ya zamto zai iya karanta wannan izun a take ba shakku,  sai dai wani ikon Allah. Da yake Alqur'ani cike yake da mu'ujiza. 

3. MAI JAGORA:
Dole ne mai son ingantaccen hadda ya zamo yana da mai JAGORA wanda zai dinga sauraron karatunsa, ya tunatar da shi idan ya yi kuskure, sannan ya masa gyara a inda ya dace. Kuma abin so shi ne ya zamo mai JAGORA yana da ilimin Tajweed ko da bai haddace Alqur'ani ba, amma da za a samu wanda ya haddace da yafi.

4. HAKURI:
Dole ne mai haddar Alqur'ani ya zamo mai haƙuri, musamman wajen kiyaye lokacin karatunsa. Domin sau da yawa Shaiɗan zai yi ta bijiro masa da abubuwan sha'awa ko son zuciya da zasu iya shagaltar dashi. Toh dole ya yi haƙuri ya kau da kan sa game da haka. Ko kuma wani lokaci ya yi ta karatun amma haddar ta ki zama,  nan ma sai ya yi haƙuri ya ci gaba da karantawa har sai ya ji haddar ta zauna sannan ya yi ƙari. Saboda a yayin da yake maimaici don haddar ta zauna, tabbas ana rubuta mishi ladaddaki akan ko wani harafi da ya furta. Don haka kada ya yi baƙin ciki yana tunanin ko karatun shi bai shiga ba.  Idan kuma yaro ne, sai mai jagora ya haƙura ya yi ta maimaita mishi har sai ya ji karatun ya zauna kafin ƙarin. 

To Idan mutum ya kiyaye ƙa'idojin can na sama guda hudu (4) 👆👆👆👆, Sai ya riƙe wasu guda hudun (4), waɗanda sune kamar:

1. AZKAAR:
Ya kasance ya kiyaye yin azkar na safe da yamma, misalin wanda ke cikin littafin hisnul-muslim. Sannan kuma ya yawaita addu'a kan Allah ya sawwake mishi haddar Alqur'ani. 

2. SAURARON SAUTIN KARATUN ALQUR'ANI:
Yana da kyau matuqa mai hadda ya dinga sauraron sautukan karatun Alqur'ani daga bakin masana karatun Alqur'ani kamar su Shaikh Minshawee, Hausary, da sauran su. Hakan na matuqar taimakawa wajen kiyaye wasula, kara karfin hadda, taimakawa wajen bibiyan ma'ana da kuma daɗaɗa sautin karatu. Manzon Allah (SAW) shi kan shi ya kasance yana sauraron karatun Alqur'ani wajen sahabbansa, kuma tabbas ya ce duk wanda ba ya rera (daɗaɗa sautinsa yayin karanta) Alqur'ani, ba ya tare da mu. 

3. BINCIKEN HADDA:
Babu abin da ke zaunar da hadda kamar sabo da Alqur'ani. Shi binciken hadda yana taimakawa matuqa wajen sabo da Alqur'ani. Yana da kyau a duk lokacin da dalibi ya ba da hadda a yi masa binciken hadda ko da ja daya ne idan babu lokaci.

4. KYAUTATA ƊABI'A 
An tambayi uwar muminai, Aisha, Allah ya yarda da ita, game da ɗabi'un manzon Allah (SAW) sai tace ɗabi'un sa shi ne Alqur'ani. 
Ma'ana, duk umarnin da Alqur'ani ya yi tabbas ya na yin shi, haka kuma duk hanin da  Alqur'ani ya yi, ba ya aikata shi.

Toh haka ake son musulmi musamman mai haddar Alqur'ani ya kasance ɗabi'un sa ya zamo Alqur'ani. Domin su ne zaɓaɓɓu a cikin bayin Allah kuma suna da wata daraja ta musamman a wajen Allah (SWT). Ko yaushe sai a dinga tunatar da ɗalibin hadda akan kyautata ɗabi'a. 

Ya Allah ka sanya Alqur'ani ya zamo hujja a gare mu ba akan mu ba.🙏🙏🙏

Post a Comment

Previous Post Next Post