KIBADA_GUDUMUWA_GURIN_KULA_DA_MIJINKI.Kina matar aure yana da ƙyau ƙwarai, da zarar kin ga mijinki ya yunƙura zai fita nemo abinci sai ki biyoshi kina mai yi masa rakiya har zaure ko ƙofar fita daga gida.

#KIBADA_GUDUMUWA_GURIN_KULA_DA_MIJINKI.

Kina matar aure yana da ƙyau ƙwarai, da zarar kin ga mijinki ya yunƙura zai fita nemo abinci sai ki biyoshi kina mai yi masa rakiya har zaure ko ƙofar fita daga gida.
Kina me dafa kafaɗarsa kina cewa ya kai masoyina da Allah Ya haɗamu, ina matuƙar kaunarka a cikin ruhuna da raina, ina maka fatan Allah Ya baka sa'ar fitar nan da za ka yi, kuma ina roƙonka dan Allah dan girman Allah ka taimaka ka nemo abinci na halas.

In kuma Allah Ya ƙaddara ba ka samu ba, toh kar ka damu ka dawo kawai, domin mu dai za mu iya haƙuri da juriya da yunwa da wahalar duniya, amma ba za mu iya haƙuri da azabar wutar lahira ba.

Wannan ita ce hanyar da matan musulmai magabata suka bada gudunmawa wajen tsare mazajensu daga auka ma cin haram da kuma taimakawa wajan gina al'umma ta ƙwarai.

Saboda haka, mace tana iya bada gudunmawa a kowane zamani yadda za a samu ingantacciyar rayuwa

ALLAH ya azurta mu da mace tagari masu tarin albarka ya bamu halat yayi muna tsari da haramun komai karancinta.

Post a Comment

Previous Post Next Post