ALALOMIN SANKARAN MAMA (NONO) DA INDA MACE ZATA DUBA KO TANA DA CIWON DA KANTA.(PLEASE SHARE)

ALALOMIN SANKARAN MAMA (NONO) DA INDA MACE ZATA DUBA KO TANA DA CIWON DA KANTA.
(PLEASE SHARE)
Idan mace tana da ciwon sankaran mama wato Breast Cancer, ga abubuwan da za iya lura a jikin ta:

(1). Zubara da jini daga kan nono.
Wanan tana samun mata masu shekara 30 zuwa 40, bari daya ko duka nonan.

(2). Zata lura da abu mai tauri cikin nono a masu kananan shekaru 15 zuwa 30.

(3). Girman nono zai karu ya zama kato yakai 20-30 cm.
Akwai ciwo da kuma canjin launin fatar gun.

(4). Zata lura nonon na kullutu kuma tana laushi kuma tana kumbura mafi yawa tana farawa ne kwana kadan yasaura zuwa lokocin Alada.

YADDA MACE ZATA DUBA KANTA A GIDA KO TANA DA CIWON
(SELF BREAST EXAMINATION)

Wannan yana magana ne yadda mace za ta gano tana da matsalon Nono kafin ta fara jawo matsala, sannan da samun nasara wajen magani.

(1). Amfani da yan yatsunki kinabin kowanegu akan nono a hankali, haka za'ayiwa dukka nonon biyu ko wacce karshen wata ) idan da canji sai a garzaya zuwa asibity.

(2). Ki tsaya a gaban mudubi ki daga hannayenki sama ko bisa kugunki. Daga nan kiduba sosai domin duba banbanci tsakanin nonanki guda biyu.
Shima idan akoi matsalar a garzaya zuwa asibiti. 

(3). Idan kin kwanta sai ki kwantar da kafadarki guda daya kan filo,ki daga hannun kafadar zuwa keyarki, sannan kisa dayan hannun danbin ko ina a hankali akan nononki domin gano ko akoi canji.

******************************************
Gobe, zamu kammala wannan topic da yanda mace zata kare kanta daga wannan ciwon da kuma yanda masu shi zasu lura da kansu kar ciwon ta kai su kasa.

Ubangiji Allah ya bamu lafiya... Ameen

(Please Share) I

Post a Comment

Previous Post Next Post