AMFANIN KHUSBARA(coriender seed) GA LAFIYA DA ADAM .Bismillahi wassalatu wassalamu ala rasulullah, khusbara yana dauke da sinadarai masu matukar mahimmanci ga lafiyar dan adam don haka wasu kasashe irinsu india suka maidashi abincinsu na yau da kullum

AMFANIN KHUSBARA(coriender seed) GA LAFIYA DA ADAM .

Bismillahi wassalatu wassalamu ala rasulullah, khusbara yana dauke da sinadarai masu matukar mahimmanci ga lafiyar dan adam don haka wasu kasashe irinsu india suka maidashi abincinsu na yau da kullum .

   KADAN DAGA CIKIN AMFANINSA.

* Yana magance dukannin cutar da ta shafi fata irinsu tau-tau,kefsi,kanzuwa,pimples,kaikaiyin jiki da sauransu.
 
 YADDA AKE AMFANI DASHI :Sai asamu garin khusbara kwaba da zuma ashafe jiki dashi bayan minti 15 sai a wanke haka za'a rinkayi har tsawon sati guda.

*Yana magance kurajen baki idan aka tafasashi ana kuskura baki dashi safe da yamma.

*Yana kara yawan gashi da tsawo dasakashi baki idan aka hada garinsa da man gashi ana shafara agashi sau biyu duk sati.

*Yana narkar da abinci kuma yana bude kafofin jin idan aka jikashi ana shansa kullun da safe kafin a karya.  

* Yana manganin sanyin jiki da mura idan ana barbadawa a abinci mai dumi.

*Yana ciwon suga (diabities) idan na kijikashi da ruwa litre daya ashanye ayini daya ana fara shansa kafin a karya haka bayan an karya har litre dayan ya kare.

*Yana kashe kwayoyin cuta kowani iri (bacteria) sai ayi yajin garinsa ko kuma ahada garinsa da curry arinka cinsa a abinci ko sallad.

*Domin cutukan da suka shafi ido ko yanar ido sai ajika khusbara arinka wanke ido dashi safe idan an tashi daga bacci da dare kafin a kwanta bacci.

*Domin magance ciwon ciki ko mara na mata a lokacin Al'ada  sai asamu cokali biyu na garin kusbara da sugar(sukari) cokali daya sai a tafasa da ruwa litre daya ya tafasa sosai sai asha da dumi duminsa wallahu ta'ala a'alam.
        
  sirrin rike miji

Post a Comment

Previous Post Next Post