ILLOLI GUDA ASHIRIN DA BASIR (DAN KANOMA) KE HADDASAWA.Basir ko kuma ince Dan kanoma wanda a Turance ake kira da "DYSENTERY" yana haddasa illoli da dama kamar haka :

ILLOLI GUDA ASHIRIN DA BASIR (DAN KANOMA) KE HADDASAWA.

Basir ko kuma ince Dan kanoma wanda a Turance ake kira da "DYSENTERY" yana haddasa illoli da dama kamar haka :

 

1.TSUWAR HANJI (INTESTINAL DISTURBANCE).Zaka rinka jin hanjin cikinka na yawan tsuwa akowane lokaci.

 

2.KUMBURIN CIKI :Cikinka zai kumbure saboda toshewar hanji a sanadin dattin ciki da yawaitar girman kwayoyin cuta da rashin samun damar abinci ya yi saurin narkewa.

 

3.YAWAN TUSA (FREQUENT FLATUELENCE) : Zaka rinka yawan fitarda iska akai akai,wani iskan sai ka ce wanda ya ci mosai.

 

4.ZAFIN JIKI DA CIWON KAI : Jikinka zai rinka zafi ga kuma yawaitar ciwon kai wanda baya jin magani kamarsu analgesic.

 

5.RASHIN CIN ABINCI KA KOSHI : Basir na haddasa maka kaji baka iya cin komai,kusan komai ka ci sai kaji ba dadi.Take ka koshi.

 

6.YAWAN ZUWA TOILET: Basir kan sa kayi ta yawon zuwa toilet,idan kaje kuma kayi ta faman yunkur da nisha sai zafin musiba da fitar majina ko jini dan tsirit.

 

7.RAMEWA : Basir kan sa ka rame kamar mai ciwon qanjamau.

 

8.CIWON GABOBIN JIKI : Basir kan haddasa ciwon jiki da kowace ga6a ta jiki.

 

9.TASHIN ZUCIYA : Sai kaji kamar kayi amai,kana ta faman zubarda yawu.

 

10.FITAR BAYA : Duburarka zata fito waje (basir mai tsiro)

 

11.CIWO A CIKIN DUBURA : Sai kaji matsanancin ciwo ka kasa tsayawa ko zama.

 

12. DAUKEWAR SHAWA : Namiji yakasance kamar baima balaga ba,ita kuma mace batama san meye biyan bukata ba,duk tabi ta bushe ba ni'ima ba wata gamsarwa.

 

13. KAIKAYIN DUBURA : Basir kansa dubura ta tsage ga zafi da fesowar kuraje.

 

14.KURAJE GA MATSE MATSI : Basir kan haddasa irin haka amma mutane da dama suna tinanin kamar sanyi ne,to na sanyi ya sha banban dana basir.Dan na sanyi akan ga zubar farin ruwa masu yauqi da wari kamar danyen kifi.

 

15. YANA MURDE HANJI : Ta yanda zai haifarda ru6ewar hanji da sauran cutukan ciki.

 

16. BAYAN GIDA MAI TAURI : Yana haddasa bayan gida mai tauri kamar duwatsu,kamar kashin dabbobi.

 

17.Basir na kawo ciwon baya.

18.Basir na haifarda (LIVER ABCESS)

19.Basir na haifarda Brain abcep,sai yakasance kamar ka kuwata.yana ma haukata Dan-adam.

20.Yana hude hanji (intestinal ulceration,ga zafin ciki kamar mai ulcer)

GARGADI : Mutane a kula ba a ko'ina ake ganin maganin basir a shafukan sada zumunta kaman whatsapp,Facebook,da makamantansu a dauka aje ana sha ba,da dama na sha ganin wasu hade hade marasa asali suna bada magani ga mutane wai su jarraba.

Duk rashin lafiyar dake damunka to ka nemi maganinta a inda ya dace ga wanda ya kamata.

Allah yabamu lafiya

Post a Comment

Previous Post Next Post